Alhazan Jihar Kaduna 2 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya Ana Haramar Dawowa Gida
- Allah ya yi wa ƙarin Alhazai biyu daga jihar Kaduna rasuwa yayin da ake shirye-shiryen fara jigilar dawowa gida Najeriya
- Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kaduna ce ta tabbatar da haka, ta kuma bayyana sunayen waɗanda suka rasu
- A gobe Talata, 4 ga watan Yuni, 2023, ake sa ran za'a fara kwaso alhazai zuwa gida bayan kammala aikin hajjin bana
Kaduna - Ƙarin Alhazan Najeriya biyu daga jihar Kaduna sun riga mu gidan gaskiya bayan kammala aikin Hajjin bana 2023 a ƙasa mai tsarki.
Mai taimakawa na musamman ga shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna, Ibrahim Giwa, ne ya tabbatar da rasuwar Alhazan ga wakilin jaridar Daily Trust a Makkah.
Ya bayyana sunayen mamatan da Bashir Umar Sambo daga ƙaramar hukumar Kubau da Sulaiman Abubakar (Unguwan Lalli) daga ƙaramar hukumar Igabi duk a cikin jihar Kaduna.
A kalamansa ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Hukumar jin daɗin alhazai na takaicin sanar da rasuwar Sulaiman Abubakar Unguwan Lalli, mai lamba KD 086 TRK daga ƙaramar hukumar Igabi da Bashir Umar Sambo, mai lamba KD 318 KB daga ƙaramar hukumar Kubau."
"Wannan ya ƙara yawan mahajjatan Kaduna da muka rasa a ƙasa mai tsarki, zuwa yanzun Alhazan mu huɗu sun kwanta dama. Muna rokon Allah ya sanya su a Aljanna kuma ya karɓi shahadarsu."
Alhazai sun fara haramar kamo hanya zuwa gida Najeriya
Haka zalika ya ƙara da cewa a halin yanzu, shirye-shirye sun yi nisa na fara jigilar Alhazai zuwa gida Najeriya.
Yayin da yake taya ɗaukacin Alhazai murna bisa kammala aikin Hajjin bana da ake sa ran ta zama karɓaɓɓa, ya shawarce su da su tattala ragowar kuɗaɗensu har zuwa ranar komawa gida.
Hadimin shugaban hukumar ya ce tuni aka fara rabawa mahajjatan manyan jakunkuna masu nauyin kilogram 32.
Daga ƙarshe ya buƙaci duk alhajin da wani abu nasa ya ɓata ya garzaya Sakatariyar hukumar jin daɗin Alhazai da ke Makka ya yi bayani.
Wani mazaunin ƙaramar hukumar Igabi ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa tabbas sun yi babban rashin mutum kirki, wanda kowa ya san bai da matsala da kowa.
Khalid Abdurrahman ya faɗa wa wakilinmu ta wayar salula cewa tare su ke sallar Jumu'a da marigayi Alhaji Sulaiman Abubakar a garinsu.
A kalamansa ya ce:
"Marigayin yana kusa da garin mu ne, kusa da jaji amma duk sati a nan yake Sallar Jumu'a. Bayan samun labarin rasuwarsa na yi kokarin kiran wani ɗan garinsu amma ban same shi ba."
"Gaskiya a sanin da na yi mashi mutumin kirki ne, kuma mutum ne na kowa, ma'ana bai da matsala."
Hajjin Bana: An Bayyana Ranar Da Alhazan Najeriya Za Su Fara Dawowa Gida Daga Saudiyya
A wani rahoton na daban kuma Alhazan Najeriya da suka gudanar da aikin Hajjin bana za su fara dawowa zuwa gida Najeriya ranar Talata 4 ga watan Yuli.
Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Makudan Kudade, Ya Daukar Musu Muhimman Alkawura 3
Shugaban kwamitin kula da harkokin jiragen sama na hukumar jindaɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Injiniya Goni Sanda, shi ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki.
Asali: Legit.ng