"Ana Min Barazanar Kisa": Asari Dokubo Ya Fallasa Masu Son Ganin Bayansa
- Asari Dokubo, tsohon shugaban tsageran Niger Delta, ya bayyana cewa ana yi masa barazanar raba shi da duniya
- Dokubo ya bayyana cewa ana turo da barazanar ne ta saƙon waya (SMS), inda aka turo saƙonnin masu yawan gaske
- Dokubo dai ya kwanto wa kan shi kura ne bayan bayyanar wani bidiyonsa inda ya yi kalamai masu kaushi akan wata ƙabila a ƙasar nan
Awka, jihar Anambra - Alhaji Mujahid Dokubo-Asari, wani ɗan gwagwarmaya daga ƙabilar Ijaw, ya bayyana cewa ya samu saƙonni da yawa daga wajen wasu ƴan Najeriya waɗanda suka yi masa barazanar ɓatar da shi daga duniya.
Dokubo ya ce suna masa barazanar ne saboda matsayarsa kan wasu abubuwa da suka shafi ƙasar nan.
Yayin da ya ke magana kai tsaye a Facebook a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli, wanda Legit.ng ta saurara, Dokubo-Asari ya bayyana cewa waɗanda su ke turo masa waɗannan saƙonnin na ƙoƙarin firgita shi ne da zubar da jini.
"Na fi ƙarfin a bani tsoro": Dokubo-Asari
A yayin da yake aikewa da saƙon gargaɗi ga irin waɗannan mutanen, Dokubo-Asari ya ce ya fi ƙarfin a tsoratar da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
"Su Inyamurai lokacin da mutanensu ke jan faɗa, ba za su tsawatar musu ba, lokacin da wanda suka takala ya mayar da martani sai su fara maganganun ƙarya. Kuna tunanin za ku iya tsoratar da ni? Yanzu kun fara ko. Ku bari a kai mu fagen daga ni da ku."
"Za su zo shafina su kira no da alade, su kira ƴaƴana ƴaƴan alade. Za su ce za su halaka ni. A wasu ranakun, ina samun dubunnan saƙonni: 'Sai mun kashe ka, sai mun yanka ka, sai mun ci naman ka'. Wai kuna tunanin za ku iya bani tsoro ne?"
An Matsawa FG Lamba Ta Cafke Dokubo Asari
A wani labarin kuma, ƙungiyar ƙare haƙƙin ɗan Adam ta HURIWA ta taso gwamnatin tarayya a gaba kan sai an cafke Alhaji Mujahid Dokubo Asari.
Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne bayan bayyanar bidiyon tsohon shugaban tsageran Niger Delta yana barazanar kakkaɓe Inyamurai.
Asali: Legit.ng