Hajji: Likitoci Sun Bayyana Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Saudiyya Yayin Da Fiye Da 40,000 Suka Yi Jinya

Hajji: Likitoci Sun Bayyana Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Saudiyya Yayin Da Fiye Da 40,000 Suka Yi Jinya

  • Likitocin alhazai a birnin Makkah sun bayyana jimillar 'yan Najeriya da suka rasa rayukansu da kuma marasa lafiya
  • Shugaban likitocin, Dakta Usman Galadima shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli a Makkah
  • Ya ce akalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu yayin da fiye da mutane 40,000 suka kamu da rashin lafiya a kasar

FCT, Abuja – Jimillar mutanen da suka rasa rayukansu a hajjin bana ya kai mutane 13 yayin da mutane 41,632 suka kamu da rashin lafiya a Saudiyya.

Shugaban likitocin alhazan, Dakta Usman Galadima shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli a Makkah.

Likitocin sun bayyana yawan mutanen da suka mutu a Saudiyya da kuma wadanda suka kamu da rashin lafiya
Mahajjata Yayin Aikin Hajji A Saudiyya. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Ya ce sun kula da marasa lafiya 25,772 lokacin Arfa yayin da suka kula da mutane 15,680 a Makkah da Madinah kafin Arfa, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Watakila Tsofaffin Ministocin Buhari Su Dawo Cikin Ministoci da Tinubu Zai Nada

An bayyana yawan mutanen da suka rasu a Saudiyya da jihohinsu

Yayin da ya ce mutane bakwai sun rasa rayukansu kafin Arfa, inda ya bayyana yawan wadanda suka mutun a jihohi kamar haka:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akwai jihohi guda biyu da mutane biyu suka mutu a ko wacce, sannan jihohi shida da birnin Tarayyar Najeriya Abuja aka samu mutum dai-dai.

Jihohin sun hada da: Kaduna (2) da Osun (2) da Plateau (1) sai Borno (1) da Lagos (1) da kuma Yobe (1) da Benue (1) sai birnin Tarayya Abuja (1).

Hukumar ta bayyana ranar da za ta fara jigilar Alhazai zuwa Najeriya

Dakta Usman ya ce jiragen yawo suma sun samu akalla mutane uku da suka rasa rayukansu, cewar rahotanni.

Ya yi kira da a dauki matakin hana tsoffi da kuma marasa lafiya zuwa Jamarat wurin da ake jifan shaidan saboda cunkoso.

Kara karanta wannan

Jika da kaka: 'Yan Najeriya sun yi ca, suna ta magana kan bidiyon wasan Tinubu da jikokinsa

Kwamishinan Hukumar Alhazai ta kasa, Goni Sanda ya ce za su fara jigilar maniyyata zuwa Najeriya a ranar 4 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agusta.

Hajji: Jimami Yayin Da Maniyaciyyar Abuja Ta Riga Mu Gidan Gaskiya A Saudiyya

A wani labarin, Hukumar Alhazai a Abuja ta sanar da rasuwar daya daga cikin maniyyata aikin hajji a Makkah yayin gudanar da ibada a Saudiyya.

Hukumar ta ce marigayiyar mai suna Hajiya Amina Yunusa ta rasa ranta ne yayin aikin hajji a kasar Saudiyya.

Daraktan hukumar a birin Tarayya, Malam Abubakar Evuti shi ya bayyana rasuwar a ranar Juma'a 30 ga watan Yuni a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.