Atiku da Peter Obi Na Bata Lokacinsu, Za Su Rasa Tsuntsu da Tarko a Kotu, Inji Sanatan Jam’iyyar APC
- Tsohon Sanata Surajudeen Ajibola Bashiru ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC za su yi nasara a kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa
- Bashiru ya ce irin karar da jam’iyyar Labour ta gabatar a kan Tinubu ta faru a shekarar 1999, kuma kundin tsarin mulki ya ce duk mutumin da aka taba samu da laifi zai tsayawa takara ne kadai bayan shekaru goma
- Sanatan ya ci gaba da cewa jam’iyyar PDP da Labour da Atiku Abubakar da Peter Obi ba su tabbatar wa kotu yadda suka lashe zaben ba da gwararan dalilai
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tsohon sanatan Osun ta Tsakiya, Surajudeen Ajibola Bashiru, ya bayyana cewa kotun sauraran kararrakin zabe za ta bai wa shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyyar APC nasara.
Da yake magana kan hasashen sakamakon hukuncin kotun, Sanatan ya caccaki jam’iyyun Labour da PDP da ‘yan takararsu, Peter Obi da Atiku Abubakar inda ya bayyana cewa sun kasa bayyana wa kotu yadda suka lashe zaben bana.
SRJ ya bayyana yadda Tinubu zai doke Atiku da Obi a kotu
Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Western Sprint, Sanatan ya bayyana cewa hatta shaidun jam’iyyun adawa sun tabbatar da cewa an gudanar da zaben bana cikin gaskiya da adalci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hakazalika, ya ce Atiku da Obi sun kasa gabatar da wata shaidar rashin adalci da ya tabbata an yi kamar yadda suke ikirari.
Ya ce halarci zaman kotu a ranakun Talata da Laraba, 20 da 21 ga watan Yuni, inda yace bai ga wani abu mai tasiri da zai kai ga kwace kujerar Bola Tinubu ba.
Batun Tinubu da harkallar kwaya
Hakazalika, ya yi tsokaci game da zargin da su Atiku da Obi suka gabatar kan cewa an taba tuhumar Tinubu da harkallar kwaya.
Ana So a Kunno Sabon Wuta: An Bukaci Tinubu Ya Ajiye Wike Sannan Ya Nada Wani Shaharren Dan Siyasar Ribas Mukamin Minista
Ya kuma bayyana cewa, ai an tuhumi Tinubu ne da harkallar kwaya shekaru kusan 30 da suka gabata, don haka ya cika ka’idar tuhuma da kundin tsarin mulkin kasa ya bayar na shekara 10.
Tinubu ya dagawa Turawa EU yatsa kan rahoton zaben 2023, ya caccake su
A wani labarin, kunji yadda gwamnatin Najeriya ta caccaki kungiyar tarayyar turai kan yadda ta ba da rahoton karshe game da zaben 2023 da aka gudanar.
A cewar gwamnati, rahoton yana cike da kuskure da son rai, don haka ta yi watsi dashi gaba dayansa.
Ba wannan ne karon farko da gwamnatin Najeriya ke samun rashin fahimtar juna da kungiyoyi da kasashen turai ba.
Asali: Legit.ng