An Shiga Matukar Damuwa da Jimami Yayin da Dalibin Ajin Karshe Na Likitanci a ABU Ya Rasu

An Shiga Matukar Damuwa da Jimami Yayin da Dalibin Ajin Karshe Na Likitanci a ABU Ya Rasu

  • Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya yi wa wani dalibin likitanci a jami’ar ABU mai suna Usman Sani Baba rasuwa bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Kungiyar Daliban Likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello sun yi jimamin rashin wannan matashin dalibi, inda suka nuna alhininsa kan rasuwarsa
  • Yabo ne dai ya biyo daga abokai, dangi, da furofesoshin da suka karantar dashi, inda suke tunawa da tasirin rayuwarsa kuma suka mika ta'aziyya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zaria, jihar Kaduna – Usman Sani Baba, dalibin ajin karshe a fannin likitanci a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, jihar Kaduna ya rasu.

An bayyana rasuwar Baba ne a wata sanarwa da aka fitar a shafin Twitter na kungiyar daliban likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar daliban, Umar Mustapha Kareto da majiyar Legit.ng ta gani, dalibin jami’ar ta ABU da ke dab da kammala karatun likitanci ya rasu ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli bayan gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Bayan An yi Rashin Wani Babban Likita a Arewacin Najeriya

Allah ya yiwa dalibin likitanci a ABU rasuwa
Dalibin da Allah ya dauke ransa yana dab da kammala digiri | Hoto: @official_abumsa
Asali: Twitter

Usman Sani Baba ya samu shaida mai kyau, cewar Kareto

Da yake bayyana makokin rasuwar Baba, Kareto ya ce, rashin da jami’ar ta yi na mamacin lamari ne mai zafi har ga iyalansa, abokan karatunsa, da kuma farfesoshinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Kareto:

“Yana da kyakkyawar makoma a gabansa, kuma rashinsa ya matukar girgiza ahalinsa, abokan karatunsa, malaman jami’arsa, da duk wanda ke da alaka da karatun likitanci.
“Tabbas rashi ne mai zafi amma mun yi hakuri da sanin cewa ya yi rayuwa mai cike albarka da tasiri, za a tuna da shi da yin amfani da lokacinsa a duniya cikin hikima da amfani, ya kara da abin da ya samu a duniya amma bai rage komai ba kuma bai lalata komai ba kana ya bar abubuwa da kyau fiye da yadda ya same su.”

Daga nan, ya yi masa addu’ar Allah ya jikansa, ya kuma masa rahama da sada shi da aljannar Firdaushi.

Kara karanta wannan

Mutane 6 Sun Rasu a Borno Yayin Da Wani Bam Da 'Yan Boko Haram Suka Binne a Kan Hanya Ya Tashi

Dalibi A Jami'ar Al-Azhar Ya Rasu Yana Sujjada Yayin Sallah

A wani labarin, Ahmed El-Sharkawy ya shafe kwanaki uku ba tare da an gan shi a tsangayar koyar da ilmin likitanci ta Jami'ar Al-Azhar wacce ke da reshen a Assiutba inda yake karantar likitanci.

Abokansa wanda suke karatu tare sun ziyarci gidansa da ke rukuni na biyu na ginin gidajen jami'ar, inda suka tarar da kofarsa a rufe, don haka suka sanar da 'yan sanda, inda suka bude kofar da karfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.