'Yan Najeriya Sun Yi Martani Mai Daukar Hankali Ga Bidiyon Tinubu da Jikokinsa Suna Wasan Jika da Kaka
- Seyi, daya daga cikin ‘ya’yan shugaban kasa Bola Tinubu ya yada bidiyon shugaban kasa na wasa da jikokinsa
- A cikin faifan bidiyon da ya saka a Instagram, an ga shugaba Tinubu a zaune yana wasa da jikokinsa 2 da ke tsaye
- An yada bidiyon mai kayatarwa ne a ranar Asabar, 1 ga Yuli, wanda ke nuna cewa lamarin ya faru ne a lokacin bikin Sallah
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
‘Yan Najeriya sun shiga martani kan faifan bidiyon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana wasa da jikokinsa, Noella da Bolatito.
Bidiyon wanda Seyi Tinubu ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya nuno shugaba Tinubu yana rike da jikokinsa guda biyu a lokacin da yake zaune akan kujera.
Seyi ya rubuta:
"A yammacin yau Noella da Bolatito (BAT jnr) sun shafe lokaci mai kayatarwa tare da kakansu @officialasiwajubat @layaltinubu
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kakanni na da dadi da ban sha'awa, suna ba da kulawa, labarai masu ban sha'awa da nuna kauna."
‘Yan Najeriya sun mayar da martani kan bidiyon Tinubu inda yake wasa da jikokinsa
'Yan Najeriya sun mayar da martani ga kyakkyawan bidiyon da aka yada a ranar Asabar, 1 ga watan Yuli.
Wani fitaccen mai gabatar da shiri a gidan talabijin na TVC, Morayo Afolabi-Brown, ya bayyana lamarin a matsayin "marasa farashi".
Wani mai kuma a Instagram, Olotaofficial ya tambayi ko zai iya canza kaka da Bolatito:
"Karamin yaro mu yi canza kaka mana."
Tolgate_dbull ya rubuta:
"Ka yi tunanin yadda yara za su yi abin ban dariya @seyitinubu. Zai iya zuwa makaranta a tambaye shi wanene shugaban Najeriya. Kada ka yi mamaki idan yaron ya rubuta KAKANA @officialasiwajubat."
Wani dan Najeriya, Akeemgbadamosi ya rubuta:
"Babanmu da Jikokinsa. Allah Ta'ala Ya sauwaka maka lamurra @officialasiwajubat domin ka kai #Nigeria zuwa ga tudun tsira!"
Tinubu ya gana da sarkin Legas
A wani labarin, kunji yadda Bola Tinubu, shugaban Najeriya ya kai ziyara ga Oba na Legas a ranar 1 ga watan Yuli.
Wannan ziyara na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar ya kai ziyara jiharsa ta Legas a lokacin bikin Sallah.
Bisa al’ada, shugabanni a kasar nan kan ziyarci jihohinsu a lokutan bukukuwan Sallah ko kirsimeti da ma sauran bukukuwa.
Asali: Legit.ng