Wani Basaraken Kasar Mexico Ya Angwance Da Kada a Wani Kasaitaccen Biki Da Aka Gudanar

Wani Basaraken Kasar Mexico Ya Angwance Da Kada a Wani Kasaitaccen Biki Da Aka Gudanar

  • Basaraken wani karamin gari a kasar Mexico mai suna Victor Hugo Sosa ya auri Kada
  • Sosa ya angwance da amaryarsa kada wacce aka yi wa ado irin na amare kuma mutanen gari sun hallara
  • Wannan aure da aka kullawani daddaden al'ada ne don kawo yalwa da wadata ga kauyen

Basaraken wani karamin gari a Kudancin kasar Mexico ya angwance da wata macen kada a al'adance domin kawowa mutanensa ci gaba mai kyau.

Victor Hugo Sosa, Sarkin San Pedro Huamelula, wani gari a Tehuantepec isthmus na kasar Mexico, ya auri wata kada mai suna Alicia Adriana, domin farfado da wata al'ada ta iyaye da kakanni, rahoton Vanguard.

Auren basarake da kasa
Wani Basaraken Kasar Mexico Ya Angwance Da Kata a Wani Kasaitaccen Biki Da Aka Gudanar Hoto: Reuters
Asali: UGC

Yadda aka yi shagalin bikin basarake da kada

Sosa ya dauki alwashin yin gaskiya ga dabbar wacce mutanen garin ke kira da "gimbiyar yarinya."

Kara karanta wannan

Yadda Magidanci Ya Kange Matarsa Tare Da Hana Ta Abinci Na Tsawon Shekaru Biyu a Wata Jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin shagalin bikin, an jiyo sosa yana cewa:

"Na yarda da daukar nauyin ne saboda muna son juna. Wannan shine abun da ya fi komai muhimmanci. Ba za a iya yin aure ba tare da so ba...Na yarda da auren gimbiyar yarinya."

An tattaro cewa aure tsakanin mutum da kada mace ya faru a nan a shekaru 230 da suka wuce don tuna ranar da wasu kungiyoyin yankin biyu suka samu zaman lafiya ta hanyar aure.

Al'ada ya nuna cewa an shawo kan rikice-rikice lokacin da wani sarki Chontal, wanda a yanzu magajin gari ya maye gurbinsa, ya auri wata gimbiya daga kungiyar Huave, wacce kadar ta wakilta.

Kafin shagalin biki, an dauki kadar zuwa gida-gida don mazauna yankin su dauke ta a hannunsu sannan su yi rawa da ita. Kadar na sanye da koriyar siketi, kanta daure da kayan adon mata masu kyau.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fitaccen malamin addini a Najeriya ya fadi a filin jirgin sama saboda tsananin rashin lafiya

An daure bakin kadar wanda ke nuna karara don kada ta kai farmaki ne.

Daga bisani, sai aka sanya mata farin kaya irin na amare sannan aka dauke ta zuwa wajen taron domin sanya albarka.

Duk a cikin shagalin biki, Joel Vasquez, wani mai kamun kifi a yankin ya jefa ragarsa da bayyana fatan garin cewa auren na iya kawo nasara wajen kama kifaye masu kyau, don wadata, daidaito da kuma zaman lafiya.

Bayan daurin auren, basaraken ya taka rawa da amaryarsa inda aka sanya masu wakokin gargajiya.

"Muna farin ciki saboda mun yi murnar hadewar al'adu biyu. Mutane sun gamsu,” Sosa ya fada wa AFP.

Ragon Sallah ya kawo rikici tsakanin mata da miji

A wani labari na daban, wani magidanci ya koka kan yadda matarsa ta daina yi masa magana da shiga harkarsa saboda bai yi mata ragon Sallah.

Magidancin wanda ya bayyana cewa basussuka sun yi masa yawa a ka ya ce matar ta girka wa yaransu abinci duk saboda rashin ragon layya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng