Tashin Hankali Yayin da Fitaccen Fasto, Chibuzor Ya Fadi Shirim a Filin Jirgin Sama, an Zace Dashi Asibiti
- Rahoton da muke samu ya bayyana yadda wani fitaccen malamin addinin Kirista ke cikin matsanancin halin rashin lafiya
- Ya zuwa yanzu, an ce an kwantar dashi a wani asibiti, inda ake neman jama’a su sanya shi a addu’ar Allah ya bashi lafiya
- Ba a bayyana zahirin abin da ya faru dashi ba, amma ana fargabar rashin lafiya ne da ya kai ga kwnatar dashi nan take
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Najeriya - A ranar Juma’ar da ta gabata ne faston da ya kafa cocin Omega Power Ministries, Chibuzor Gift Chinyere ya fadi shirim a wani filin jirgin saman da a bayyana ba saboda wani ciwon da ake fargabar na damunsa.
Malamin na coci ya shiga tereren kafafen yada labarai a shekarun baya yayin da ya dauki wasu yara ma’aikatan gidan cin abinci ya tura su karatu kasar waje.
A baya-bayan nan, ya bayyana daukar nauyin iyayen wata dalibar da aka kashe a Sokoto bisa zarginta da cin mutuncin manzon tsira; Annabi Muhammadu SAW.
Sai dai, an yi ta korafe-korafe kan cewa, kyautar da ya yi alkawarin yiwa iyayen Deborah ta samu cikas, inda daga baya ya karyata hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ga faston a kwance a kasa a filin jirgin sama
A wani hoton da ya yadu a kafar sada zumunta, an ga lokacin da faston ke kwance a kasa kafin daga bisani aka tattara shi zuwa asibiti.
A bidiyon da aka yada a Facebook, an ce malamin dan asalin jihar jihar Ribas tabbas baya cikin hayyacinsa a filin jirgin saman.
Sakon da aka wallafa hade da bidiyon ya ce:
“Mu kokarta don Allah mu sanya Ubanmu a cikin addu’o’inmu.”
A bangare guda, mabiya mashabar da magoya baya malamin na ci gaba da zabga addu’o’i a kafafen sada zumunta.
Fasto ya ba iyayen Deborah gida
A wani labarin, Chibuzor Chinyere, babban faston cocin Omega Power Ministry, (OPM), ya mika kyautan gida da mota ga iyalan Deborah Samuel Yakubu, dalibar da aka kashe a Sokoto kan batanci ga Annabi (SAW), The Cable ta rahoto.
An yi wa Deborah, dalibar aji na 2 a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari a Sokoto duka da sanduna kafin nan aka cinna mata wuta a harabar makarantar a ranar 12 ga watan Mayu.
Duk da cewa wasu sun yi tir da kisar da aka yi mata a Najeriya da kasashen ketare, an yi zanga-zanga a Sokoto na neman ganin an sako wadanda ake zargi da hannu a kisar ta.
Asali: Legit.ng