Magidanci Ya Saki Daya Daga Cikin Matansa, Ya Mayar Da Dayar Gida Saboda Matsin Tattalin Arziki
- Wani mai siyar da kayan wuta a birnin Warri ya saki matarsa ta biyu sannan ya tura matarsa ta farko zuwa Sokoto saboda matsin tattalin arziƙin da ake ciki
- Ya bayyana cewa matansa sun fahimci hukuncin da ya yanke inda ya ce rayuwa sai ta fi sauki a garinsu fiye da Warri
- Ya ɗora alhakin rashin cinikin da yake yi akan ƙara farashin man fetur inda ya ce ba zai sake aure ba ko komawa wajen iyalansa har sai abubuwa sun farfaɗo
Wani magidanci mai shekara 43 a duniya, Yunusa Ahmad, ɗan jihar Sokoto ya bayyana yadda ya saki matarsa ta biyu sannan ya tura matarsa ta farko da ƴaƴansa huɗu zuwa garinsu saboda halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar nan.
Ahmad, wanda yake siyar da kayan wuta a babbar kasuwar Warri a jihar Delta, ya gayawa jaridar Tribune cewa ya kwashe shekara uku a Warri, amma ba zai iya ci gaba da iya sauke nauyin da ke kansa ba saboda yadda rayuwa ta yi tsada.
"Ina auren mata biyu, amma saboda halin da ake ciki yanzu a ƙasar nan, dole na saki ɗaya daga cikinsu" A cewarsa.
Matar da ya saka ta fahimci hukuncin da ya yanke
Ya bayyana cewa matarsa ta biyu da ya sallama basu haihuwa ba sannan ba ta ji haushin sakin da ya yi mata ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ta fahimci halin da muka tsinci kan mu a ciki." A cewarsa.
Ya bayyana cewa matarsa ta farko wacce suka haifi ƴaƴa huɗu tare, ta amince ta koma Sokoto tare da yaran, inda a cewarsa rayuwa ta fi sauƙi a can.
A kalamansa:
"Kula da ragowae ɗayar ma ya zama jan aiki, hakan ya sanya na mayar da ita tare da yaran zuwa gida. Rayuwa ta fi sauƙi a can fiye da nan."
Ya koka kan yadda ciniki ya ragu sosai a wajen kasuwancinsa
“Ta Ce Ba Za Ta Biya Ni Ba Har Sai Mun Yi Ido Hudu”: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Masoyiyarsa Baturiya a Bidiyo
Ahmad ya koka cewa ƙarin kuɗin farashin man fetur ya taɓa masa kasuwanci inda yanzu sam babu wani ciniki sosai.
"A baya akwai riba sosai a kasuwancin, saboda abubuwa na da sauƙi, amma hanzu ba haka abubuwan su ke ba" A cewarsa.
"Abinda a baya da za a siyo a N2,000 sannan a siyar a N3, 000, yanzu ko a farashin da ake siyar da shi ba zaka samu ba, saboda komai ya yi tsada.
Ahmed ya ce baya da shirin yin wani auren ko dawo da iyalansa zuwa Warri har sai har sai abubuwa sun daidaita.
Magidanci Ya Kai Surikansa Kara a Kotu
A wani labarin kuma, wani magidanci ya kai iyayen matarsa ƙara a gaban kotu bisa zargin cewa sun ɗauke masa mata ba tare da izninsa ba.
Magidancin dai ya kai ƙarar ne a gaban wata kotun shari'ar musulunci domin neman a bi masa haƙƙinsa.
Asali: Legit.ng