Uzodimma Ya Gana Da Sanwo-Olu Kan Rikicin Yarbawa Da Inyamurai a Lagas

Uzodimma Ya Gana Da Sanwo-Olu Kan Rikicin Yarbawa Da Inyamurai a Lagas

  • Daga karshe Gwamna Hope Uzodimma da Gwamna Babajide Sanwo-Olu sun shiga tsakani a rikicin Yarbawa da Inyamurai a jihar Lagas
  • Shugabannin biyu sun gana a gidan gwamnati domin magance zazzafan rikicin da ke tsakanin yan kasuwa Inyamurai da yan Lagas
  • An tattaro cewa Gwamna Sanwo-Olu ya ba gwamnan jihar Imo tabbacin cewa za a ba inyamurai yanci a jihar Lagas

Lagos, Ikeja - Ana tsaka da zazzafan rikici tsakanin yan kasuwa Inyamurai da Yarbawa a jihar Lagas, Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo ya ziyarci Gwamna Babajide Sanwo-Olu don magance rikicin da kawo karshensa.

A cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu a ranar Juma'a, 30 ga watan Yuni, gwamnonin na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun cimma matsaya domin ci gaba da samawa inyamurai yanci a Lagas.

Kara karanta wannan

Sanatan Da Ya Hana Gwamna Yin Sallar Idi Ya Yi Karin Haske Kan Lamarin Da Ya Faru a Tsakaninsu

Gwamna Hope Uzodimma ya gana da Gwamna Sanwo-Olu
Uzodimma Ya Gana Da Sanwo-Olu Kan Rikicin Yarbawa Da Inyamurai a Lagas Hoto: Governor Hope Uzodimma
Asali: Facebook

Da yake magana jim kadan bayan ganawar tasu, Gwamna Uzodimma ya nuna kwarin guiwa kan matakin da gwamna Sanwo-Olu ya dauka na tabbatar da kariya da tsaron inyamurai a jihar Lagas.

Sanwo-Olu ya ba da tabbacin kare rayuka da dukiyoyin Inyamurai

Saboda haka, ya karfafawa Inyamurai gwiwar komawa bakin kasuwancinsu ba tare da tsoron cin zarafi ba domin dai ya samu tabbaci daga dan uwansa Gwamnan jihar Lagas cewa babu wata manufa da za a kawo da nufin cutar da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana yayin hirar, Gwamna Sanwo-Olu na jihar Lagas ya ba Gwamna Uzodimma da gaba daya tawagar inyamurai tabbacin jajircewarsa don ba Inyamura da dukkanin kabilun da ke Lagas kariya.

Ya bukaci karin hadin gwiwa tsakanin yankunan da zaman lafiya tsakanin gaba daya kabilu.

Mataimakin kakakin majalisar wakilai na kasa, Ben Kalu da sauran manyan shugabannin Inyamurai a kasuwa sun yi wa Gwamna Uzodimma rakiya.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Ya Kori Hakimai, Masu Unguwanni Ana Shirye-Shiryen Hawan Sallah

HURIWA ta ba gwamnatin tarayya awanni 72 ta kama Asari Dokubo kan barazanar da ya yi wa inyamurai

A wani labari na daban, mun ji cewa kungiyar HURIWA ta ba gwamnatin tarayya awanni 72 ta kama tsohon shugaban tsagerun yan bindigar Neja Delta dan tawaye Mujahid Asari-Dokubo.

Hakan ya kasance ne saboda wani bidiyon Dokubo da ya yadu inda ya yi wa inyamurai barazana yayin da yake rike da bindigar AK-47.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng