Har Yanzu Dangote Ne Mutumin Da Ya Fi Kowa Kudi a Afrika Yana Da Dala Biliyan 15.6

Har Yanzu Dangote Ne Mutumin Da Ya Fi Kowa Kudi a Afrika Yana Da Dala Biliyan 15.6

  • Aliko Dangote, shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a Afrika a cikin jerin masu kudi na Bloomberg, inda yake da dala biliyan 15.6
  • Attajirin na Najeriya, ya kasance rike da kambun wanda ya fi kowa kudi a Afrika tsawon shekaru 12 da suka gabata
  • Shugaban masana'antun Dangote ya koma matsayi 111 a duniya, bayan samun dala miliyan 20.7 da ya yi a cikin sa'o'i 24

Shugaban rukunin masana'antu na Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ci gaba da rike kundin attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika, duk da faduwar darajar Naira a kan dala da ta durkusar da mafi yawan hannayen jari a Najeriya.

A cewar Bloomberg, Dangote ya na da adadin kudade har dala biliyan 15.6 kuma shi ne attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tasa Keyar Matashi Mai Shekaru 18 Zuwa Gidan Dan Kande Kan Zargin Satar Akuya, Ya Samu Rangwame

Dangote ne ya fi kowa kudi a Afrika
Aliko Dangote ne attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika. Hoto: Bloomberg
Asali: UGC

Dangote ne dan Najeriya daya tilo a cikin jerin masu kudin duniya

Aliko Dangote ne kadai dan Najeriya a cikin jerin sunayen mutane 500 da suka fi kowa arziki a duniya, kuma ya kasance mutumin da ya fi kowa kudi a Afrika na tsawon shekaru 12 da suka gabata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban abokin kasuwancinsa a Najeriya, Abdul Samad Isiyaka Rabiu, ya fice daga jerin sunayen bayan da ya yi asarar kimanin dala biliyan 2.8, sakamakon faduwar darajar Naira.

Rukunin masana'antu na Dangote, shi ke da mallakin babban kamfanin samar da siminti a Afrika, wato Dangote Cement, wanda nan ne babbar hanyar samun kudaden attajirin.

Har ila yau, kamfanin yana da samar da sukari, gishiri, taki, da kayan abinci.

A kwanakin baya ne Dangote ya kaddamar da katafariyar matatar mai ta dala biliyan 19, wacce ita ce mafi girma a Afrika.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Haɗu da Shugaban Kasar Benin, Ya Taɓo Batun Iyakoki da Kasuwanci

Sauran 'yan Afirka da ke cikin jerin masu kudin a duniya

Sauran ‘yan Afrika da ke cikin jerin masu kudi 500 na Bloomberg sun hada da Johann Ruppert, wanda ya hau kan Dangote a jerin attajiran Forbes a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afrika da dukiyar da ta kai dala biliyan 13.3.

Nicky Oppenheimer dan kasar Afrika ta Kudu, Nassef Onsi Sawiris na kasar Masar, Natie Kirsh na Afrika ta Kudu da kuma Naguib Onsi Sawiris na kasar Masar na cikin jerin masu kudin na Bloomberg.

A ranar Laraba, 28 ga watan Yuni, 2023, Dangote ya hau daga na 122 zuwa 111 a jerin masu kudin, bayan samun kusan dala miliyan 20.7 a cikin sa’o’i 24.

Wannan dai shine babban ci gaban da Dangote ya yi a cikin makonni biyu tun bayan da ya sauka daga matsayi na 76 a farkon watan Yuni.

Mutanen da suka fi kowa kudi a duniya

Kara karanta wannan

“Aiki Ya Yi Kyau”: Matashi Ya Kammala Hadadden Gidansa, Ya Zuba Kujeru Yan Waje Da Kayan Alatu

Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, da hamshakin attajirin nan dan kasar Faransa, Bernard Arnault, su ne manyan attajirai a duniya.

Elon Musk na da arzikin da ya kai dalar Amurka biliyan 231, a yayin da Bernad Arnault ke da dala biliyan 197, a lokacin da ake rubuta labarin nan.

Masu take musu baya sune, mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos, da kuma mai kamfanin Microsoft, Bill Gates, wadanda ke da dala biliyan 151 da kuma dala biliyan 130, bi da bi.

Shettima ya gana da Dangote da Bill Gates a Abuja

A wani labari da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi wata ganawa da Aliko Dangote, da kuma babban attajirin nan, Bill Gates a Abuja.

Ganin dai na cikin ayyukan da shugaban gidauniyar Melinda and Gates foundation ya gabatar a ziyarar kasashen Najeriya da Nijar da ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng