CAN Ta Yi Allah Wadai da Kisan Mahauci, Usman Buba a Jihar Sakkwato
- CAN ta yi Allah wadai da kisan wani mahauci, Usman Buba bisa zargin ya yi kalaman ɓatanci a jihar Sakkwato
- A ranar Alhamis, shugaban CAN na ƙasa, Archbishop Daniel Okoh, ya ce ba su goyon bayan tada yamutsi da kuma ɗaukar doka a hannu
- A kwanakin da suka gabata wasu mutane suka yi ajalin Usman a mahautar Sakkwato bisa zargin ɓatanci, lamarin da ya bar baya da ƙura
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Sokoto state - Ƙungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta yi Alla wadai da kisan gillan da aka yi wa Usman Buba, wani mahauci da ake zargin ya yi ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
Shugaban CAN na ƙasa, Archbishop Daniel Okoh, shi ne ya bayyana haka ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni, 2023 a birnin tarayya Abuja, kamar yadda daily trust ta rahoto.
Ya kuma miƙa sakon ta'aziyya da jaje ga iyalai, yan uwa da abokan arziƙin mamacin, wanda a cewarsa masu tsattsauran ra'ayin addini suka yi ajalinsa.
Bamu goyon bayan ɗaukar doka a hannu - CAN
A kalamansa, shugaban CAN ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A rahoton da muka samu, kisan gilla aka yi wa Usman Buda bisa zargin ya yi kalaman ɓatanci. CAN ta yi imani da 'yancin yin addini kowane iri da kuma bayyana abinda mutum ya yi imani da shi."
"Saboda haka mun yi hannun riga da duk wani kalar tada zaune tsaye da ɗaukar doka a hannu da sunan Addini."
"Wannan abun takaicin da ya faru (a Sakkwato) ya ƙara nuna cewa akwai buƙatar ƙara inganta hakuri da addinai, zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mutanen ƙasar nan."
Ya ce ƙungiyar CAN ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen fafutukar kare 'yancin kowane ɗan ƙasa, ba tare da duba addinin da mutum ya yi imani da shi ba, kamar yadda Puch ta ruwaito.
Idan baku manta ba a makon da shige, wasu mutane suka lakaɗa wa Usman Buba duka har lahira bisa zargin ɓatanci ga Annabi SAW. Da yawan shaidu sun ce bai yi abinda ake zarginsa ba.
Kada Ku Ci Bashin Ragon Layya, Malamin Addini Ya Gargadi Al'ummar Musulmi
A wani rahoton na daban kuma Fitaccen malamin addinin Musulunci ya yi gargadi ga al'ummar Musulmi kan runtumo bashi don yin layya.
Sheikh Muhammad Adewoyin ya ce cin bashi don yin layya ba abin burgewa ba ne illa karin wahalhalu da mutane ke kakaba wa kansu.
Asali: Legit.ng