Yanzu Yanzu: Buhari Ya Karyata Batun Neman Tinubu Ya Daina Binciken Emefiele Da Sauransu
- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karyata rade-radin da ake yi cewa ya nemi shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da binciken tsoffin yan majalisarsa
- Wata sanarwa dauke da sa hannun tsohon kakakin tsohon shugaban kasar, Garba Shehu, ta ce labarin ba gaskiya bace face kanzon kurege
- Shehu ya jadadda burin tsohon ubangidan nasa na son kauracewa yin katsalandar a harkokin gwamnati mai ci a yanzu
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi martani ga rahotannin cewa shi ya nemi kada shugaban kasa Bola Tinubu ya binciki yan majalisarsa.
A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, Garba Shehu, tsohon kakakin tsohon shugaban kasar, ya yi watsi da rahoton cewa Buhari ya fada ma shugaban kasa Tinubu ya daina binciken da ke gudana na wasu yan majalisarsa.
Buhari bai nemi Tinubu ya dakatar da binciken yan majalisarsa ba, Garba Shehu
Shugaban kasa Tinubu da magabacinsa, Buhari sun yi ganawar sirri a birnin Landan, yayin ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Amurka a ranar Litinin, 26 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya rubuta a shafin nasa:
"ABUN DA BUHARI BAI FADA MA SHUGABAN KASA TINUBU BA.
"Idan za a yarda da soshiyal midiya, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman kada magajinsa, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya binciki wasu tsoffin jami’an gwamnatinsa. Labarin kanzon kurege ne, kada mu tattauna shi ko ba shi karfi. Wannan labaran karya be, kuma bai fi haka ba. Abun godiya, babu wani mutum baya ga shugabannin biyu a dakin da suka gana, saboda haka babu wanda ke wajen da zai kwaso rahoton tattaunawarsu. Kamar yadda yake, tsohon shugaban kasar baya son yin katsalandar domin kada ya janye hankalin sabuwar gwamnati. Ya zabi komawa Daura yana fatan jin shirun da yake sowa kansa amma ya lura cewa ba haka abun yake ba, baki na ta tururuwa a safe, rana da dare, ya fice zuwa waje mai nisa. Burinsa ne neman a bari ya samu hutun da yake bukata, sannan kuma don gwamnatin Tinubu ta samu yanayin da ya dace don aiki da cimma alakawaran da suka dauka.”
Kalli wallafar a kasa:
Shugaba Tinubu ya sa labule da Buhari a Landan
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a birnin Landan.
Yayin da ba a san takamaiman abun da suka tattauna a kai ba, wasu hadimai sun wallafa hotunan shugabannin biyu a soshiyal midiya.
Asali: Legit.ng