Shugaba Tinubu Zai Gana da Sarakunan Jihar Ogun Yau Alhamis
- Sakon gayyata ya riski shugabanni da magoya bayan jam'iyyar All Progressive Congress (APC) reshen jihar Ogun
- Wannan gayyata na zuwa ne yayin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya shirya shiga jihar ranar 29 ga watan Yuni, 2023 domin gana wa da Sarakuna
- Hadimin gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, Babatunde Olaotan, ne ya bayyana haka ranar Laraba, 28 ga watan Yuni, 2023
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ogun state - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shirya kai ziyara Abeokuta da Ijebu-Ode a jihar Ogun ranar Alhamis (yau) 29 ga watan Yuni, 2023.
Shugaban kasan zai ziyarci Awujale kuma babban Sarkin ƙasar Ijebu, Oba Sikiru Adetona a Ijebu-Ode da kuma Alake na Egbaland watau Sarkin ƙasar Egba, Oba Adedotun Gbadebo a Abeokuta.
Meyasa Bola Tinubu zai gana da Sarakunan Ogun?
Hadimin gwamnan Dago Aboidun na Ogun, Babatunde Olaotan, ne ya bayyana haka a wasiƙar gayyata da ya tura wa shugabannin APC da magoya baya ranar Laraba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar Daily Trust ta kawo a rahotonta cewa Mista Olaotan bai faɗi maƙasudin wannan ziyara da shugaban ƙasan zai kai jihar Ogun ba.
Takardar gayyatar ta ce:
"Gwamna Dapo Abiodun na gayyatar ku zuwa wurin tarban mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu GCFR wanda zai kawo mana ziyara gobe 29 ga watan Yuni (Yau) a Abeokuta da Ijebu-Ode."
"Muna buƙatar shugabannin mu na jam'iyya, dattawa da magoya baya na mazabar Ogun ta gabas su tattaru a fadar Awujale da misalin ƙarfe 8:30 na safe domin tarba."
"Haka nan muna rokon jagororin APC, dattawa, mambobi da magoya baya daga mazaɓun Ogun ta tsakiya da Ogun ta yamma su haɗu a fadar mai martaba Alake da ƙarfe 10:30 na safe."
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa yanzu haka shugaba Bola Tinubu na mahaifarsa jihar Legas domin murnar zagayowar babbar Sallah a kalandar musulunci (Eid El Kabir).
Shugaban INEC Ya Fi Gwamnan CBN Yi Wa 'Yan Najeriya Illa, Bula Galadima
A wani rahoton na daban kuma Buba Galadima ya yi kira ga shugaban kasa Tinubu ya kori Farfesa Mahmud Yakubu daga mukamin shugaban INEC.
Ya ce abinda Farfesa Yakubu ya aikata, ya zarce laifukan da dakataccen gwamnan CBN , Godwin Emefiele, ya yi wa 'yan Najeriya muni.
Asali: Legit.ng