Eid-el-Kabir: Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Yan Najeriya Su Yi Wa Shugabanni Addu'a

Eid-el-Kabir: Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Yan Najeriya Su Yi Wa Shugabanni Addu'a

  • Sarkin Musulmi ya buƙaci yan Najeriya su dage da yi wa sabbin shugabanni addu'o'i kuma su mara musu baya
  • Jim kaɗan bayan dawowa daga wurin sallar idi babba, Alhaji Sa'ad Abubakar ya ce lokacin siyasa ya wuce, yanzu lokaci ne na shugabanci
  • Mathew Hassan Kuka ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Sokoto State - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya ja hankalin 'Yan Najeriya game da abinda ya dace su maida hankali wajen yi wa sabbin shugabannin da aka rantsar.

Sultan na Sakkwato ya yi kira ga ɗaukacin 'yan Najeriya da su dage da yi wa sabbin shugabannin da aka rantsar addu'o'i kuma su mara musu baya don su kafa gwamnatin da zata amfani al'umma.

Kara karanta wannan

Miliyan 1 Na Ke Ware Wa Jami'an Kan Hanya Yayin Jigilar Shanu Daga Arewa Zuwa Kudu, In Ji Isiaka

Sarkin Musulmai, Alhaji Sa'ad Abubakar na III.
Eid-el-Kabir: Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Yan Najeriya Su Yi Wa Shugabanni Addu'a Hoto: NTA News
Asali: Facebook

Channels tv ta rahoto cewa Sarkin ya yi wannan kira ne a fadarsa da ke birnin Sakkwato jim kaɗan bayan dawowa daga sallar idi babba (Eid-El-Kabir) ranar Laraba, 28 ga watan Yuni, 2023.

Bayan haka Sarkin Musulmin ya kuma ƙara kira ga hukumomin tsaro da su ƙara zage dantse su nunka kokarin da su ke wajen yaƙar 'yan ta'adda da sauran waɗanda suka hana zaman lafiya a kasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lokacin siyasa ya wuce inji Sultan

Bugu da ƙari, Basaraken ya kuma roƙi sabbin shuwagabannin da suka karɓi ragamar ƙasar nan a matakai daban-daban cewa su rungumi kowa su yi aiki tare ba tare da duba banbancin siyasa ba.

Alhaji Sa'ad Abubakar III ya faɗa wa shugabannin su tuna cewa lokacin siyasa ya wuce, yanzun lokacin jagoranci ne.

Da yake nasa jawabin ga yan jarida a fadar sarkin Musulmi, Bishof na Cocin Catholic Diocese, Mathew Hassan Kukah, ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Tinubu, ya tabbatar da kariya ga rayuka da dukiyoyin kowane ɗan ƙasa.

Kara karanta wannan

Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya

"Muna Bukatar Yin Sadaukarwa" Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Bayan Gama Sallar Idi

A wani rahoton na daban kuma Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya ja hankalin 'yan Najeriya jim kaɗan bayan kammala Salla a masallacin idi a jihar Legas.

Tinubu ya kuma jaddada bukatar haɗa kai da ƙaunar juna kana ya roƙi 'yan Najeriya su jingine duk wani banbancin addini ko ƙabila sannan su yi hadaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262