Kitimurmura: Waliyyin Amarya Ya Sace Sadakin Amarya Ana Shirin Daura Aure

Kitimurmura: Waliyyin Amarya Ya Sace Sadakin Amarya Ana Shirin Daura Aure

  • An tafka abun kunya a wajen wani ɗaurin aure a jihar Kano bayan waliyyin amarya ya sace kuɗin sadaki
  • Waliyyin amaryar dai ya fakaici ido ya ƙunshe kuɗin sadakin amaryar cikin aljihunsa inda ya bar mutane suka yi cirko-cirko ana tunanin ina kuɗi suka shiga
  • Asiri ya tonu ne bayan da aka yanke shawarar a bincike duk mutanen da ke a wajen inda kwatsam kawai sai ga kuɗi a aljihun waliyyin amarya

Jihar Kano - Ana zargin wani ɗan'uwan amarya wanda zai bayar da aurenta (waliyyi) da sace kuɗin sadakinta ana dab da ɗaura aurenta a yankin Kurna cikin ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa lokacin da lamarin ya auku, an bar mutane sun yi cirko-cirko suna jiran a ɗaura auren yayin da sadakin ya yi ɓatan dabo.

Kara karanta wannan

Amarya Da Kannen Mijinta Sun Kubuta Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane a Jihar Kwara

Waliyyin amarya ya sace kudin sadaki a Kano
Waliyyin amaryar ya sace kudin sadakin ne a masallaci Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin, Sunusi Dan Mamman, ya bayyana cewa bayan an kwashe dogon lokaci ana jira, mutanen wajen sun amince da a lalube duk waɗanda ke a wajen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gano kuɗin sadakin a aljuhun waliyyin amaryar

A lokacin ne kwatsam aka yi kiciɓus da kuɗin sadakin a cikin aljihun waliyyin amaryar. Waliyyin ya bayyana cewa bai san yadda aka yi kuɗaɗen suka samu wurin zama ba a aljihunsa.

"Bayan an karɓo kuɗin, an kori waliyyin amaryar daga masallacin saboda ba zai iya zama wakilin amaryar ba. Sai aka sanya ƙaninsa a matsayin wanda zai tsaya mata sannan aka ci gaba da ɗaurin auren."

Da aka nemi sanin jin ko an cafke waliyyin amaryar bayan an kammala ɗaurin auren, majiyar sai ya kada baki yace babu wanda ke da masaniyar hakan saboda ba a ga motsinsa ba a wajen bayan an kammala ɗaurin auren.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Farmaki Wasu Kauyuka a Jihar Bauchi, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah Masu Yawa

Ango Ya Nemi Saki a Kotu Kwana 2 Bayan Daurin Aure

A wani labarin na daban kuma, wani sabon ango ya fusata inda ya nemi kotu da ta datse igiyar aurensa da amaryarsa bayan ya kamata da aikata wani mummunan laifi.

Amaryar dai ta sanya hannu ne ta rama marin da mahaifiyar ango ta yi mata wanda hakan ya fusata ango ya ce sai sun rabu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng