Da Dumi-Dumi: Mummunar Gobara Ta Tashi a Gidan Shugaban Kungiyar Kwadago Ta Kasa, An Tafka Asara
- Wata gobara mai ban mamaki ta lalata gaba ɗaya gidan shugaban ƙungiyar ƙwadago na ƙasa da ke a jihar Legas, Joe Ajaero
- Rahotanni sun nuna cewa gaba ɗaya ginin ya ƙone ƙurmus a dalilin gobarar, inda ba ta bar komai ba a cikin gidan
- Ajaero, wanda ya fara shugabancin NLC a watan Fabrairun 2023, ba ya cikin ƙasar nan lokacin da gobarar ta auku
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ikeja, jihar Legas - Gidan shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, da ke a jihar Legas, ya kama da wuta.
A cewar rahoton jaridar Vanguard, gobarar ta auku ne a ranar Talata, 27 ga watan Yuni inda ta laƙume komai da ke a cikin gidan.
Gobara ta tashi a gidan shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) Joe Ajaero
Gobarar mai ban mamaki ta fara ne daga saman rufin gidan sannan sai wata iriyar ƙara ta biyo baya wacce mutanen gidan suka ɗauka cewa ta dabbobin da ke kiwo ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai, ƴan mintuna kaɗan baya. hakan sai ginin ya kama da wuta ta ko ina yayin da mutanen gidan suka kama tseren tsira da rayuwarsu.
An tattaro cewa duk da ƙoƙarin da mutanen unguwar da ƴan kwana-kwana suka yi domin takaita gobarar, lamarin ya fi ƙarfinsu.
Ajaero ya yi magana kan gobarar da ta auku a gidansa
A lokacin da gobarar ta auku, Ajaero ba ya cikin ƙasar nan inda ya yi tafiya zuwa birnin Geneva na ƙasar Switzerland.
Lokacin da aka tuntuɓe shi domin jin ta bakinsa, sai ya ce ya godewa Allah da babu wanda ya rasa ransa a gobarar.
Da aka tambayi shi ko yana tunanin cewa hari ne aka kawo masa, sai ya ce aikinsa a matsayin shugaban ƙungiyar ƙwadago yana tare da haɗari mai yawa, amma bai yi maganar ko akwai waɗanda ke yunƙurin ganin bayansa ba.
Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwa a Jihar Yobe
A wani labarin kuma, wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar jihar Yobe, wacce ke a birnin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Gobarar ta tashi ne a ɓangaren masu sana'ar yadi na kasuwar ta Bayan Tasha, inda ta laƙume kayan miliyoyin naira.
Asali: Legit.ng