Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Shafe Kwanaki a Kasashen Waje

Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Shafe Kwanaki a Kasashen Waje

  • Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan shafe kwanaki da dama a ƙasar Faransa da birnin Landan
  • Rahoto ya nuna cewa jirgin shugaban kasan ya dira a filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da ƙasa Murtala Muhammed a jihar Legas
  • Gwamnq Babajide Sanwo-Olu da wasu manyan jiga-jigan gwamnati sun je wurin tarbo Tinubu, wanda ya sauka da karfe 5:02 na yamma

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos State - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan shafe kwanaki a birnin Farisa, na ƙasar Faransa inda ya halarci taron kuɗi na duniya kana ya wuce Landan.

The Nation ta rahoto cewa shugaban Tinubu ya sauka a sashin shugaban kasa na filin jirgin Murtala Muhammed a jihar Legas da misalin karfe 5:05 na yammacin yau Talata, 26 ga watan Yuni, 2023.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu Da Sauran Manyan Jiga-Jigan Da Suka Tarbi Shugaba Tinubu a Legas

Shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo gida Najeriya.
Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Shafe Kwanaki a Kasashen Waje Hoto: Thenation
Asali: UGC

Ya samu tarba daga tawagar magoya bayansa waɗanda suka jima a filin sauka da tashin jiragen sama na ƙasa da ƙasa tsawon awanni suna dakon isowarsa.

Shugaba Tinubu y zarce ya sauka a jihar Legas ne domin shagulgulan babbar Sallah (Eid-el-Kabir) a mahaifarsa, karo na farko tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya na 16.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Waɗanda suka je tarben Tinubu a filin jirgin sama

Daily Trust ta tattari cewa gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya je tarban shugaban kasa Tinubu, wanda ake tsammanin zai shafe kwanakin hutun Sallah a gida.

Gabanin saukar jirgin shugaban kasa, sabon mai bada shawara kan tsaron kasa (NSA), Nuhu Ribaɗu, ya je sahin shugaban ƙasa na filin jirgin domin yi wa Tinubu maraba da dawowa.

Ribaɗu, wanda shugaban kasa ya naɗa a matsayin NSA tare da hafsoshin tsaron Najeriya, ya kama aiki a daidai lokacin shugaba Tinubu baya cikin ƙasa.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Shugaba Tinubu Ya Yi Ƙus-Kus da Buhari a Landan, Gaskiya Ta Bayyana

Shugaba Tinubu Ya Gana da Buhari a Birnin Landan, Bayanai Sun Fito

A wani labarin na daban kun ji cewa Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon shugaban kasan da ya gabace shi, Muhammadu Buhari a birnin Landan na kasar Burtaniya.

Idan baku manta ba shugaba Tinubu ya bar Najeriya a ranar 20 ga watan Yuni, 2023 domin halartar taron kwana biyu kan kuɗi wanda ya gudana a birnin Farisa, ƙasar Faransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262