Babbar Sallah: Gwamnan Jihar Jigawa Ya Kara Hutun Sallah Har Zuwa Ranar Juma'a

Babbar Sallah: Gwamnan Jihar Jigawa Ya Kara Hutun Sallah Har Zuwa Ranar Juma'a

  • Gwamna Umar Namadi ya bayyana ranar Juma'a, 30 ga watan Yunin 2023 a matsayin ranar hutu a jihar Jigawa
  • Namadi ya bayyana cewa hutun na ranar Juma'a an bayar da shi ne domin ci gaba da murnar shagulgulan babbar Sallah
  • Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da shugaban ma'aikatan jihar, Alhaji Hussaini Ali Kila, ya rattaɓawa hannu

Jihar Jigawa - Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ƙara hutun shagulgulan babbar Sallah har zuwa ranar Juma'a, 30 ga watan Yunin 2023.

Gwamna Namadi ya bayyana ranar Juma'a a matsayin ranar hutu domin ci gaba da murnar shagulgulan bikin babbar Sallah, rahoton Nigerian Tribune ya tabbatar.

Gwamnan jihar Jigawa ya kara hutun babbar Sallah
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi Hoto: Jigawa State Government, Nigeria
Source: Facebook

Shugaban ma'aikatan jihar, Alhaji Hussaini Ali Kila, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Eid El Kabir: Portable Mai Wakar Zazu Ya Hargista Intanet Bayan Nuna Shanu 5 Da Raguna 2 Da Ya Siya Don Shagulgulan Sallah

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana ranar Juma'a, 30 ga watan Yunin 2023 a matsayin ranar hutu domin murnar shagulgulan bikin babbar Sallah sannan tana taya Musulman jihar Jigawa da Najeriya baki ɗaya murnar zagayowar babbar Sallah."

Gwamnan ya nuna fatan cewa addu'o'i da sadaukarwar da za a yi a lokacin bikin Sallah za su dawo da zaman lafiya da haɗin kan da ake buƙata a jihar Jigawa

"Muna fatan cewa addu'o'i da ayyukan alkhairi za su kawo zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a jihar Jigawa."

Ranar Laraba Za a Yi Idin Babbar Sallah

A ranar Laraba, 28 ga watan Yunin 2023 ne za a gudanar da Idin babbar Sallah a faɗin Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu domin murnar shagulgulan bikin Babbar Sallah, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Eid El-Kabir: Shugaba Tinubu Ya Ayyana Ranaku 2 Don Hutun Babban Sallah

Gwamnan Jihar Neja Ya Tuna Da Fursononi a Lokacin Shagalin Sallah

A wani labarin na daban kuma, gwamnatin jihar Neja karkashin jagorancin gwamna Muhammed Bago ta biya tarar naira miliyan N20m domin ceto fursunoni 80 daga gidajen gyaran hali 8 da ke faɗin jihar.

Gwamnatin jihar ta ji ƙan Fursunonin ne a wani yunkuri na rage cinkoson da gidajen yari suka yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng