“Kalli Abun da Suka Siyar Mun”: Mai Sana’ar Gwanjo Ta Fashe Da Kuka Bayan Bude Sinkin N250k Da Ta Bude

“Kalli Abun da Suka Siyar Mun”: Mai Sana’ar Gwanjo Ta Fashe Da Kuka Bayan Bude Sinkin N250k Da Ta Bude

  • Wata matashiya yar Najeriya ta fashe da kuka bayan ta biya kudade masu yawan gaske don siyan sinkin gwanjo
  • A cewar matar wacce ta karaya, ta kashe zunzurutun kudi har N250,000 wajen siyan sinkin gwanjon kayan yara kanana
  • Abun takaici, bayan ta bude sai ta ga cewa kayayyakin da ke ciki bai kai darajar wannan kudi da ta biya ba ko kusa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata yar kasuwa a Najeriya ta fashe da kuka bayan ta siya kaya da darajarsa ya kai N250,000.

Matar, wacce ke siyar da kayan gwanjo don samun rufin asiri, ta gaza boye kunar da zuciyarta ke yi bayan ta siya kaya marasa kyau.

Matashiya da kayan gwanjo
“Kalli Abun da Suka Siyar Mun”: Mai Sana’ar Gwanjo Ta Fashe Da Kuka Bayan Bude Sinkin N250k Da Ta Bude Hoto: @mzz_morel/TikTok.
Asali: TikTok

A cikin wani bidiyo da ta wallafa a TikTok, ta baje kolin kaya marasa inganci da aka bata, yayin da hawaye ke sauka a kan kuncinta.

Kara karanta wannan

“Uwar Miji Ta Ce Ba Zan Taba Haihuwa Ba”: Yar Najeriya Ta Samu Cikin Yan 3, Ta Nuna Wa Duniya

"Na siya sinkin gwajon kayan yara na UK mai nauyin 55kg kan N250k, amma ga abun da na gani a ciki da na bude shi," ta koka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da Legit.ng ta tuntube ta, ta bayyana cewa ta mayar da kayan zuwa wajen da ta siya, amma wanda ya siyar mata ya ki karba.

Ta ce:

"Ina siyar da kayan yara kamar irin wadanda ke a shafin kasuwancina @morels_closet. Saboda haka na je kasuwa don siyan sinki kamar yadda na saba don haka sai na siya sinkin N250k. Da kudin mota zuwa shagona. Da isa na shago sai na bude sannan na ga cewa duk safuna da yan kanfai ne.
"Na mayar zuwa shagon da na siya amma sun ce babu abun da za su iya yi akai. Cewa na je na siyar da su. Don haka na karaya sosai. Saboda na karbi kudade daga wajen kwastamomina da ke sha'awar siyan wannan kaya."

Kara karanta wannan

"Ban San Yadda Aka Yi Na Samu Juna Biyu Ba Tare Da Kwanciyar Aure Ba": Matar Aure Ta Gaya Wa Kotu

Jama'a sun yi martani

@jasmenes_glam ta ce:

"Ki fara dan karamin sinki na mata masu shayarwa da masu juna biyu. Ina iya ganin abun share miyau, zafunan kafa da wanduna ma."

@ayoke2008 ta ce:

"A 2009 kwastam sun karbi kayana na 450K na yi kuka kamar karamar yarinya a lokacin, duk mutumin da bai da karfin hali baya yin kasuwanci."

@hanikeola01 ta kara da cewar:

"Kasuwanci mara tabbass. Ya fi ka sari masu kyau daga masara sannan ka daura riba kadan fiye da ka siya sinki! Wannan shine kasuwanci mafi hatsari da mutum zai yi."

Kalli bidiyon a kasa:

Budurwa ta ce za ta iya marin mahaifiyarta kan miliyan N2

A wani labarin kuma, wata matashiya ta girgiza intanet bayan ta bayyana cewa za ta iya marin mahaifiyar da ta tsuguna ta haifeta a kan naira miliyan 2.

Sai dai ta ce mahaifiyar tata za ta fahimceta domin za ta dan tsakura mata daga cikin kudin idan ta dafe su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng