Sojoji Sun Bankado Gidan Da Yan Mata Ke Haihuwar Jarirai Ana Sayar Da Su Adamawa

Sojoji Sun Bankado Gidan Da Yan Mata Ke Haihuwar Jarirai Ana Sayar Da Su Adamawa

  • Rundunar sojin Najeriya ta bankado wani sansani da ake samar da jarirai ba bisa ka'ida ba a jihar Adamawa
  • Rundunar ta bayyana kama wadanda ake zargi mutum bakwai tare da 'yan mata 17 da ake tursasawa haihuwar jariran
  • Wannan matsala ta zama ruwan dare a Najeriya musamman a Kudancin kasar da akafi samun yawaitar faruwar hakan

Jihar Adamawa - Rundunar sojin Najeriya ta kai samame sansanin haihuwar jarirai ba bisa ka'ida ba da safarar mutane a jihar Adamawa.

Yayin samamen, rundunar ta kama wadanda ake zargi mutane bakwai a maboyar da kuma 'yan mata 17.

Sojoji Sun Bankado Sansanin Kyankyashe Jarirai Ba Bisa Ka'ida Ba A Adamawa
Wadanda Aka Kama A Sansanin. Hoto: WikkiTimes.
Asali: Facebook

Babban kwamandan yanki na 23, Birgediya Janar Muhammad Gambo shi ya bayyana haka ga 'yan jaridu a Yola a yau Litinin 26 ga watan Yuni.

Kwamandan ya bayyana yadda suka samu sansanin tare da 'yan mata da ake tursasawa

Kara karanta wannan

Tinubu: Tsare-Tsaren Sabon Shugaban Najeriya Na Daukar Idon Duniya – Birtaniya

Ya ce rundunar na aiki ne a bakin iyakar Najeriya da Kamaru lokacin da suka samu rahoton wannan sansani da ta'asar da ake yi, Daily Trust ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa sansanin na dauke da 'yan mata masu shekaru tsakanin 19 zuwa 21 da suka kwashe fiye da shekaru 3 ba tare da sanin 'yan uwansu ba.

Muhammad Gambo ya ce bankado wannan sansani ya kara tabbatar da karuwar safarar mutane da ake yawan samu a Najeriya, cewar Vanguard.

Ya yabawa sojojin yadda suka bankado sansanin haihuwar jariran

Ya yabawa rundunar sojin kan wannan nasara inda ya ce yana fatan wannan ya zama matakin farko na dakile wannan matsalar.

Ya ce:

"Wadanda ake zargin da kuma 'yan matan da abin ya shafa an tafi da su zuwa hedkwatar rundunar da ke Yola."

Kara karanta wannan

An Ba Abba Gida-Gida Wa’adin Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano, Cikakken Bayani

Ina Neman Afuwarku Game da Ciwon Zuciyan Da Aka Sanya Muku, Fintiri Ga Mutanen Adamawa

A wani labarin, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya nemi afuwar mutanen jihar kan kakaba musu sake zaben cike gurbi.

Fintiri ya samu nasara ne kwanaki uku bayan kwamishinan zabe, Hudu Ari ya yi kuskuren sanar da Binani a matsayin wacce ta lashe zabe.

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben jihar a ranar 18 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.