Ashsha: Dan Sanda Ya Yi Yunkurin Halaka Abokin Aikinsa, Ya Kare a Hannun Hukuma
- Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta cafke ɗaya daga cikin jami'anta bayan ya yi yunƙurin halaka abokin aikinsa
- Insfeta Moses Paul ya dai yunƙurin ɗaukar ran abokin aikinsa ne suna tsaka da bakin aikinsu a garin Kafanchan na jihar
- Ɗan sandan ne ya so halaka abokin aikin nasa ne domin ya ƙwace bindigarsa sai bai samu nasara ba bayan sauran abokan aikinsa sun kawo ɗauki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Wani Insfetan ɗan sanda a jihar Kaduna ya shiga hannun hukuma bayan ya yi ƙoƙarin halaka abokin aikinsa.
Jaridar Channels tv ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a Kafanchan cikin ƙaramar hukumar Jemaa ta jihar Kaduna.
A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige ya fitar, lamarin ya auku ne a ranar Juma'a, 16 ga watan Yunin 2023 a sansanin ƴan sandan tafi da gidanka a Kafanchan.
Rai Bakon Duniya: An Yi Babban Rashi Yayin Da Tsohon Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ya Kwanta Dama
Jalige ya bayyana cewa Insfeta Moses Paul ya yi ƙoƙarin halaka wani abokin aikinsa mai suna, Simnawa Paul, ta hanyar shaƙe masa wuya da igiya, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar kakakin wasu jami'an ƴan sanda guda biyu ne suka ceto ɗan sandan waɗanda hankalinsu ya kai kan kukan neman taimakon da ya riƙa yi.
Dalilin da ya sanya ɗan sandan ya yi ƙoƙarin halaka abokin aikinsa
Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa dalilin ɗan sandan shi ne ya ƙwace bindigar Simnawa Paul, yayin da za a ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ya bayyana cewa idan aka same shi da laifi, Insfeta Paul zai fuskanci ladabtarwa da hukuncin shari'a.
Dan Sanda Ya Bindige Dattijuwa a Adamawa
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke ɗaya daga cikin jami'anta bisa zargin bindige wata tsohuwa mai shekara 80 a duniya har lahira.
Jami'in ɗan sanda dai yaje kamen wani matashi ne wanda ɗan uwan dattijuwar ne, amma sai mutane suka hana shi shiga cikin gidan har sai ya faɗi dalilin kama shi, ana cikin haka kawai ya harba bindiga wacce ta yi ajalin tsohuwar.
Asali: Legit.ng