Karya Ta Kare: Hukumar EFFC Ta Cafke Sanata Kan Badakalar €5.7m
- Dubun wani Sanatan bogi mai aikata laifukan damfara ta cika a birnin tarayya bayan hukumomi sun yi caraf da shi
- Jami'an hukumar hana yaƙi da hanci ne suka yi caraf da Ifechukwu Tom Makwe bisa zargin aikafa laifin damfarar yanar gizo
- Makwe ya raba wata baturiya da maƙudan kuɗaɗenta har €5.7m bayan da ya fara damfararta tun a shekarar 2013 bayan sun haɗu a soshiyal midiya
FCT, Abuja - Jami'an hukumar hana cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) sun cafke wani sanatan bogi, Ifechukwu Tom Makwe, bisa zargin damfarar yanar gizo har ta €5.7m.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa, Makwe ya shiga hannu ne a unguwar Guzape cikin birnin tarayya Abuja, bayan an samu bayanan sirri kan harkokin damfarar yanar gizo da ya daɗe yana aikatawa.
A cikin wata sanarwa da hukumar EFCC ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa wanda ake zargin yana amfani da sunaye da dama da suka haɗa da Fahad Makwe, Sanata Tompolo, Tom Makwe da Dr. Bran, inda ya damfari wata ƴar ƙasar Spain maƙudan kuɗaɗe waɗanda yawansu ya kai €5.7m.
Sanatan bogin ya yi amfani da sunayen ƙarya wajen tafka damfarar
Makwe ya yi iƙirarin cewa shi jami'in hukumar bincike ta tarayya ta ƙasar Amurka (FBI) ne kuma lauyan diflomasiyya, inda ya samu nasarar damfarar matar ta hanyar amfani da sunayen ƙarya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wanda ake zargin dai ya fara damfarar matar ne tun shekarar 2013 lokacin da suka fara haɗuwa a soshiyal midiya.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa za a tasa ƙeyar wanda ake zargin zuwa gaban kotu ya girbi abinda ya shuka da zarar ta kammala binciken da ta ke gudanarwa.
EFCC Ta Kama Daliban Jami'a 19 Bisa Zargin Damfara Ta Intanet
A wani labarin na daban kuma, hukumar hana yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta baza komar bincikenta zuwa kan ɗaliban jami'a, inda ta yi caraf da mutum 19 waɗanda ake zargi da aikata damfarar yanar gizo.
Jami'an hukumar ta EFCC sun yi caraf da ɗaliban na jami'ar jihar Akwa Ibom a ɗakunan kwanansu bisa zargin aikata laifin damfara.
Asali: Legit.ng