Kano: Dubban Matasa Sun Fito Zanga-Zanga Kan Rusau Da Gwamnatin Abba Gida Gida Ke Yi

Kano: Dubban Matasa Sun Fito Zanga-Zanga Kan Rusau Da Gwamnatin Abba Gida Gida Ke Yi

  • Daruruwan masu zanga-zanga sun cika titunan birnin Kano don nuna damuwarsu kan rusau
  • Matasan sun kirayi gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf da ya janye kudirisa na ci gaba da rushe-rushen
  • An yi kiyasin tafka asarar fiye da N150bn saboda rushe-rushen da gwamnatin jihar ke yi kan duniyoyin jama'a

Jihar Kano - Masu zanga-zanga sun cika titunan birnin Kano don nuna damuwarsu kan rushe-rushen da gwamnatin jihar ta Abba Gida Gida ke yi.

Daily Trust ta tattaro cewa gwamnatin Kano ta rusa gine-gine da dama a jihar yayin da take shirin ci gaba da rushe-rushen da ke jawo asarar dukiyoyi.

Zanga-zangar kin jinin rusau ta barke a jihar Kano bayan Abba Gida Gida ya ci gaba da rushe-rushe
Dubban Matasa Sun Fito Zanga-Zanga Kan Rusau Da Gwamnatin Abba Gida Gida Ke Yi. Hoto: Intel.
Asali: Facebook

Gwamnatin ta sha fada cewa za ta ci gaba da rusau din akan shaguna ko gidajen da aka gina ko mallaka ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Rusau: Kotu Ta Taka Wa Abba Gida Gida Birki Kan Rushe-Rushen Gine-Gine A Kano

Abba Gida Gida ya ci gaba da rusau a birnin Kano

Daga cikin gine-ginen da gwamnatin ta rushe akwai tsohon otal din Daula da manyan kantuna a filin Polo da kuma filin Idi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da gwamnatin ta saka jan layi don rushe wasu gine-gine a Salanta da ke kan hanyar BUK a birnin Kano.

Da yake magana a madadin masu zanga-zangar, Kwamared Zahradeen Sani Bala ya ce ya kamata idan Abba Gida Gida ya na da wani matsala da tsohon ya kira shi ya amsa laifukansa.

Masu zanga-zangar sun nuna bacin ransu

Ya ce bai kamata gwamnan yana azabtar da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba tare da rushe duniyoyinsu.

A cewarsa:

"Idan kanada wata matsala da tsohon gwamna, ka kira shi ya amsa tambayoyi ba kawai a rinka azabtar da mutane tare da lalata duniyoyinsu ba."

Kara karanta wannan

Gwamnati Za Ta Ruguza Gine-Gine, Ta Tsallake Wuraren da Kwankwaso Ya Saida a Kano

Masu zanga-zangar suna ta daga wasu takardu da ke dauke da cewa:

"Gwamna Yusuf, wannan abin da kake yi yana korar masu zuba jari daga jihar."

Yayin da wasu ke cewa:

"Kada ka kawo mana rashin tsaro jihar mu."
"Gwamna, kabar doka ta yi aikinta."

Bayan masu zanga-zangar sun taru a otal din Daula da aka rushe, sun wuce zuwa Hedkwatar 'yan sanda don kai korafinsu.

Gwamnatin jihar ta sha alwashin ci gaba da rushe gine-gine da aka gina su ko mallakarsu ba bisa ka'ida ba don tabbatar da sauya birnin kamar yadda hukumar tsara birane ta tsara.

Kotu Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Rushe-Rushen Gine-Gine A Jihar

A wani labarin, kotu ta umarci gwamnan Kano, Abba Kabir da ya dakatar da ci gaba da rusau a jihar.

Wannan umarni na zuwa ne bayan wani mazaunin Kano, Saminu Muhammad ya shigar da kara akan shirin rushe masa shaguna.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Siyar Da Filin Da Aka Sanya Cikin Wadanda Za a Rusa, Rimingado Ya Magantu

Alkalin kotun, S.A Amobeda ya umarci gwamnan Kano Abba Kabir da ya dakatar da shirin rushe shagunan da ke kan hanyar BUK.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.