Amarya Da Kannen Mijinta Sun Kubuta Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane a Jihar Kwara

Amarya Da Kannen Mijinta Sun Kubuta Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane a Jihar Kwara

  • Wata amarya da ƙannen mijinta mata da masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Kwara sun shaƙi iskar ƴanci
  • Masu garkuwa da mutanen dai sun kutsa har cikin gidansu amaryar ne inda suka tasa ƙeyarsu zuwa cikin daji
  • An sako su ne dai bayan da aka biya kuɗin fansa har N7m ga masu garkuwa da mutanen waɗanda suka nemi a biya su N50m

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kwara - Wata amarya mai suna Rukkayat Musa da ƙannen mijinta mata guda biyu da aka sace a gidansu da ke kan titin Sarki a birnin Ilorin na jihar Kwara, sun shaƙi iskar ƴanci.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa an sako su ne bayan an biya N7m a matsayin kuɗin fansa. Miyagun da suka ɗauke su dai sun nemi da a biya N50m Matsayin kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake Bisa Kuskure, Sun Sace Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

Amarya ta kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Kwara
Sai da aka biya N7m kudin fansa kafin a sako su Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Rukkayat da sauran matan guda biyu, Hafsat da Aliyah, an sako su ne cikin dare a ranar Lahadi.

An dai yi awon gaba da su ne cikin tsakar dare a ranar Alhamis lokacin da ƴan bindiga suka kutsa kai cikin gidan da amaryar ta ke a unguwar Oniyangi akan titin Sarki a birnin Ilorin, cewar rahoton The Punch.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mijin amaryar Mr Musa, ya arce bayan masu garkuwa da mutanen sun shiga cikin gidan wanda yake na haya ne da ke a rukunin gidajen Alaya.

Ƴan sanda basu da masaniya kan lamarin

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ya bayyana cewa bai da masaniya kan lamarin.

"Ba ni da masaniya kan lamarin, babu wanda ya gaya min sace wannan sabuwar amaryar." A cewarsa.

Sai da aka biya kuɗin fansa kafin a sako su

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Farmaki Wasu Kauyuka a Jihar Bauchi, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah Masu Yawa

Amma wani ɗan'uwan amaryar wanda ya nemi da a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an sako matan ne a daren ranar Lahadi.

A kalamansa:

"Sun iso Ilorin sannan suka kira mu da misalin ƙarfe 2:00 na dare (ranar Lahadi) amma ba kyauta aka sako su ba.
"Sai da aka biya masu garkuwa da mutanen N7m a matsayin kuɗin fansa ƙasa da N50m da suka nema da farko. Ba za mu iya haɗa wannan kuɗin ba amma mun yi kuka da magiya kafin su amince da N7m wanda muka haɗa a tsakaninmu."

Ya bayyana cewa an garzaya da su zuwa asibiti domin duba lafiyarsu inda ya ƙara da cewa ba ƴan sanda ba ne suka ceto su.

'Yan Bindiga Sun Sace Manajar Banki

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun sace wata manajar banki na birnin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a gaban jami'an tsaro.

Mrs Nneka Unoka dai ta sha samun kashedin barazanar yin garkuwa da ita daga hannun ƴan bindigar, inda daga ƙarshe suka samu nasarar sace ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng