Kotu Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Rushe-Rushen Gine-Gine A Jihar

Kotu Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Rushe-Rushen Gine-Gine A Jihar

  • Wata kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta umarci gwamnatin jihar ta dakatar rushe-rushen da take
  • Saminu Muhammad wanda shi ya shigar da karar ta roki kotun da dakatar da shirin rushe shagunansa
  • Alkalin kotun, S. A Amobeda shi ya ba da wannan umarni a ranar Juma'a 23 ga watan Yuni a Kano

Jihar Kano - Wata kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta umarci gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya dakatar da ci gaba da rushe-rushe a jihar.

Wani mazaunin Kano, Saminu Muhammad shi ya shigar da karar inda ya bukaci kotun ta dakatar da gwamnan daga rushe masa shagunansa a jihar.

Kotu ta dakatar gwamnatin Kano ci gaba da rusau a jihar
Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Ci Gaba Da Rushe-rushe a Jihar. Hoto: Intel.
Asali: Facebook

Alkalin kotun, S.A Amobeda a ranar Juma'a 23 ga watan Yuni ya umarci gwamnatin jihar da ta tsagaita rushe-rushen da take yi na dukiyoyin jama'a.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Siyar Da Filin Da Aka Sanya Cikin Wadanda Za a Rusa, Rimingado Ya Magantu

Alkalin ya umarci gwamatin Kano ta dakatar da rushe-rushe

Alkalin ya yi umarnin ne musamman kan shirin rushe ginin wanda ya shigar da kara da ke lamba ta 4 da 43 akan hanyar BUK a Kano, cewar Daily Post.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga cikin wadanada ake karar akwai lauyan gwamnatin jihar da gwamnan jihar Kano da gwamnati jihar da kuma hukumar kula da birane ta Kano.

Sauran sun hada da babban sifetan 'yan sanda da kwamishinan 'yan sanda da jami'an tsaro na 'yan sanda da NSCDC da sauransu.

Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraran karar

Bayan sauraran korafi daga lauyan wanda ke karar, Farfesa Aliyu Nasiru, kotun ta dage sauraran karar zuwa 10 ga watan Yuli don ci gaba da shari'ar, Punch ta tattaro.

Daga cikin umarnin kotun na cewa:

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Abba Gida Ya Yi Makin Shaguna Da Gidajen Mai Na Miliyoyin Naira Cikin Wadanda Za a Rushe

"Wannan kotu ta ba da umarnin dakatar da wadanda ake kara da masu goya musu baya daga wuce gona da iri da shiga da kwacewa da kuma rushe kadara na wannan mai kara.
"Wanda ke lamba ta 4 da 43 a Salanta kan hanyar BUK a Kano, wanda ya na da takardar shaidar mallakar wurin mai lamba KNMLO8228 da kuma KNMLO8229 har zuwa lokacin sanar da hukuncin wannan karar."

Rusau: NITP Ta Gargadi Gwamnatin Kano Kan Tsagaita Rushe-rushe A Jihar

A wani labarin, Kungiyar masu tsara birane ta NITP gargadi gwamnatin Kano kan rushe-rushe.

Kungiyar ta ce a halin yanzu an yi asarar fiye da N120bn sakamakon rushe-rushen da gwamnatin ke yi.

Gwamna Abba Kabir ya dukufa wurin rushe-rushe da ya ce an mallake su ko gina su ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.