“Idan Rabo Ya Rantse”: Matashi Dan Najeriya Ya Buga Caca Da N10, Ya Lashe Miliyan N2
- Mutane da dama sun taya wani matashi dan Najeriya murna bayan ya yi nasarar lashe miliyan N2 daga wani gidan caca
- Ya saka N10 ne kacal wajen buga cacar inda mutane ke ganin da ya sanya sama da haka da kudin ya fi haka
- Mutumin ya fada ma masu tambayar dalilinsa na sanya kudi kadan cewa abun da zai iya yarda ya yi asara kenan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani dan Najeriya mai suna @isthatUW a Twitter ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya wallafa takardar caca da ya buga, wanda ke nuna ya ci miliyan N2.
Abun da ya ba mutane mamaki shine cewa da N10 kacal ya buga wasanni fiye da 146,000. Sa'arsa ya sa mutane yi masa tambayoyi a sashinsa na sharhi.
@isthatUW ya gode ma Allah da bai sa ya hakura ba. Mutumin ya yi martani ga mutanen da ke ganin ya yi asarar wasa ta hanyar saka kudi kadan. Ya fada masu cewa abun da zai iya yarda ya yi asara kenan.
Wasu amsu amfani da Twitter sun roke shi da ya ajiye masu lambobin cacar a gaba domin wasu ma su taki sa'a da fita daga kangin talauci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@TalentedFBG ya ce:
"Sau daya dama take zuwa ba sau biyu ba."
@The_BETMAKER ya ce:
"Wato wannan ne ainihin mai tikitin baaaba tikitinka ya yi nisa faaa amma basa saka sunanka a kai don a tayaka murnar wannan nasara taka."
@bin_gbada ya ce:
"Da N200 ya ciyo maka miliyan 40. Gaskiya Sportybet ta yi abu da wannan kananan cacar na 10-20 naira."
@desmondAlake ya ce:
"Na fahimceka dan uwa amma gaskiya baka yi kokari ba. Ka buga abun nan da naira 100 ha."
@Juliusbalaa ya ce:
"Da ka yi kokari ka sa N100 miliyan 20 kenan."
@yosoreoluwaa ya ce:
"Idan ban kurba daga wannan ni'ima ba, zan yake ka. Ka dunga ajiye lambobin sirri daga yanzu."
Rayuwar matashiya yar Najeriya da ke talla a titi ya sauya, ta koma Turai
A wani labari na daban, wata matashiya da ke tallan lemukan kwalba a Najeriya na tsawon awanni cikin zafin rana ta samu sauyi a rayuwa.
A wani mataki a bidiyon da aka wallafa a TikTok, matashiyar @sinatu26 ta nuna yadda talla na tsawon awanni ya lalata mata tafukan kafafunta. kafafuwan nata na dauke da raunuka iri-iri.
Asali: Legit.ng