Muna Kan Aikin Kawo Hanyoyin Rage Radadin Cire Tallafin Mai A Najeriya, Tinubu
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa na kokarin rage wa yan kasa zafin ciwon cire tallafin man fetur
- Yayin zama da yan Najeriya mazauna Faransa da wasu ƙasashen Turai, Tinubu ya ce dole akwai buƙatar kuɗi domin aiwatar da shirin rage raɗaɗin
- Ya kuma bayyana hanyar da ya bi wajen shawo kan ƙungiyoyin kwadugo har suka fasa zanga-zangar da suka shirya
Paris, Farance - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da cewa tuni aka gama aikin lalubo hanyoyon rage wa 'yan Najeriya raɗaɗi da ƙuncin cire tallafin man fetur.
Shugaban ƙasa ya yi wannan furuci ne yayin ganawarsa da 'yan Najeriya mazauna Faransa da wasu kasashen turai da ke maƙwaftaka da Faransa.
Jaridar The Nation ta rahoto shugaba Tinubu na cewa:
"Zamu kawo hanyoyin rage raɗaɗi amma dole sai mun samu kuɗin da zamu aiwatar da burinmu na rage wa yan kasa zafin cire tallafin a aikace."
Batun Nadin Ministoci: Fitacciyar Lauya Ta Shawarci Tinubu Ya Gujewa Jiga-Jigan Kurakurai 5 Da Buhari Ya Yi
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ko ta ya shugaban ƙasa ya shawo kan 'yan kwadugo suka fasa shiga yajin aiki?
Dangane da yadda shugaban kasa ya yi nasarar shawo kan ƙungiyoyin kwadugo suka hakura da zanga-zanga da shiga yajin aikin da suka shirya kan cire tallafin mai, Tinubu ya ce:
"Kuna buƙatar kuɗi domin rage raɗaɗi, sufuri, to me zaku fita ku yi zanga-zanga a kai? Ko dai da ku ake kashe mu raba da kuɗin tallafin fetur ɗin?"
"Idan kuka ce zaku yi zanga-zanga, nima zan fito na shiga cikinku mu yi zanga-zanga tare, da suka ji haka sai suka dakata, ba sauran wata zanga-zanga."
Idan baku manta tun a jawabin bikin rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, Shugaban Tinubu ya sanar da cewa tallafin man fetur ya tafi.
A cewarsa, gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta ware kuɗin biyan tallafin har bayan watan Yuni ba a cikin ƙunshin kasafin kuɗin 2023, kamar yadda Channels ta tattaro.
Bola Tinubu Ya Haɗu da Shugaban Kasar Benin, Ya Taɓo Batun Iyakoki da Kasuwan
A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ga gana da takwaransa na ƙasar Benin, Patrice Talon, a Faransa.
Shugaban kasar ya ce Najeriya da Benin su na bukatar juna musamman a bangarorin tsaro, kasuwanci da kula da iyakoki.
Asali: Legit.ng