An Shiga Damuwa Yayinda ‘Yan Bindiga Suka Halaka Masu Haƙar Ma’adinai 3 A Filato

An Shiga Damuwa Yayinda ‘Yan Bindiga Suka Halaka Masu Haƙar Ma’adinai 3 A Filato

  • Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane uku tare da raunata wasu biyu a wani wurin haƙar ma’adanai da ke yankin Tanjol a jihar Filato
  • Mista Rwang Tengwong, sakataren yaɗa labarai na wata ƙungiyar matasan Berom ne ya tabbatar da faruwar harin da ya da misalin karfe 11 na safe
  • Tengwong ya yi kira da a ƙara daukar matakan tsaro don kare rayuka da dukiyoyi a yankunan karkara

Jos, Plateau - Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane uku a ranar Juma’a a wani wurin hakar ma’adinai da ke kusa da Tanjol a cikin yankin Jol da ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato.

Mista Rwang Tengwong, sakataren yaɗa labarai na kungiyar matasan Berom, wacce ƙungiya ce ta al’adu da zamantakewa, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Juma’a a Jos, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Hatsabiban 'Yan Ta'adda 6 Sun Sheƙa Lahira a Arewacin Najeriya

'Yan ta'addan sun kashe mutane 3 a Filato
'Yan ta'adda sun halaka mutane 3 gami da jikkata 2 a Filato. Hoto: @Calebmutfwang
Asali: Twitter

Mutane biyu sun jikkata a harin

A cewar Tengwong, mummunan lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewa an samu ƙarin wasu mutane biyu da suka jikkata a harin, kamar yadda The Nation ta wallafa.

A kalamansa:

“Da misalin ƙarfe 11 na safe ‘yan bindigar sun kashe mutane uku tare da raunata wasu biyu a wani wurin hakar ma’adinai da ke Tanjol a yankin Jol na ƙaramar hukumar Riyom.”
"Mutanen da suka jikkata a halin yanzu na samun kulawa a wani asibiti dake yankin."

An yi kira ga gwamnati ta tsare rai da dukiyoyin al'umma

Tengwong, wanda ya bayyana harin a matsayin ɗaya daga cikin irinsa da yawa da ke faruwa a yankin.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma, musamman a yankunan karkara.

Kara karanta wannan

An Kama Saurayi Da Budurwarsa Da Suka Sayar Da Jinjirinsu Don Siyan Kwayoyi

Da aka kira Mista Alfred Alabo, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Filato a waya, bai samu damar amsa kiran ba.

Sai dai wani babban jami’i a hukumar ‘yan sandan jihar da ba a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Zulum zai ɗau ƙwaƙƙwaran mataki kan kisan manoma 8 da ISWAP ta yi a Borno

A wani labarin na daban da Legit.ng ta wallafa a baya, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya sha alwashin ɗaukar mataki mai tsauri, biyo bayan wani hari da 'yan ta'addan ISWAP suka kai a wasu garuruwa da ke jihar.

Gwamnan ya bayyana harin a matsayin abin takaici, sannan ya yi alƙawarin samar da wata ƙungiya da za ta riƙa bai wa manoman kariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng