Yanzu Yanzu: Bidiyo Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Shugaban Kasa Tinubu Ya Gana Da Yan Najeriya Mazauna Waje
- Shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu na cikin wata ganawa da yan Najeriya mazauna waje a birnin Paris, kasar Faransa
- Ganawar ta ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni ita ce ganawa ta farko da shugaban kasar ke yi da yan Najeriya mazauna waje a hukumance
- Hukumar yan Najeriya a kasar waje ta tabbatar da ci gaban a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na cikin ganawa da yan Najeriya mazauna kasar waje a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni.
Wannan shine karo na farko da shugaban kasar ke ganawa da yan Najeriya mazauna waje a Faransa, a gefen taron duniya da ke gudana a birnin Paris, NTA News ta tabbatar.
Yanzu haka Tinubu na cikin ganawa da yan Najeriya a kasar waje
Hukumar Najeriya a Faransa da hukumar yan Najeriya mazauna waje (NIDCOM) ne suka shirya taron tsakanin Tinubu da yan Najeriya mazauna waje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta tabbatar da ci gaban a wata wallafa da ta yi a shafinta na yanar gizo, tare da bidiyoyi da hotuna a Twitter a ranar Juma'a.
Wadanda suka halarci taron
Wadanda suka halarci taron sun hada da manyan masu ruwa da tsaki da Dele Alake da kuma tsohuwar shugabar hukumar NIDCOM Abike Erewa Dabiri.
Bidiyo da hotunan ganawar Tinubu da yan Najeriya a faransa ya bayyana a soshiyal midiya
Kalli bidiyo da hotunan da hukumar ta wallafa a Twitter a kasa:
"Ya kamata Tinubu ya gwada nada masanin tattalin arziki a matsayin gwamnan CBN", Dan Fafutua
A wani labari na daban, mun ji cewa an shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakatar da al'adar nan na nada ma'aikatan banki a matsayin gwamnonin babban bankin Najeriya (CBN), dadaddiyar al'adar babban bankin kasar.
Deji Adeyanju, wanda ya kasance dan fafutuka na Najeriya shine ya bayar da shawarar a wata wallafa da ya yi a Twitter a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni.
Dan fafutukar ya yi ikirarin cewa ma'aikatan banki basu san komai kan yadda ake tafiyar da harkokin tattalin arzikin kasa ba illa su din yan kasuwa ne kawai.
Asali: Legit.ng