An Shiga Damuwa, Yayin Da Gobara Ta Janyo Asarar Dukiya Mai Ɗumbin Yawa a Ogun

An Shiga Damuwa, Yayin Da Gobara Ta Janyo Asarar Dukiya Mai Ɗumbin Yawa a Ogun

  • Gobara da ta tashi a wata kasuwar masu sana'ar siyar da katako da ke Sango Ota jihar Ogun, ta yi sanadin rasa dukiya mai tarin yawa
  • Gobarar wacce ta tashi da safiyar ranar Alhamis, ta cinye shaguna da dama da ke ɗauke da kayayyaki a cikinsu
  • Duk da ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ba, wani ɗan kasuwa ya ce daga shagon siyar da katifa gobarar ta tashi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ogun - Wata mummunar gobara da ta tashi a wata kasuwar katako da ke Sango Ota jihar Ogun, ta janyo asarar dukiya mai ɗumbin yawa.

'Yan kasuwa da dama ne suka bayyana irin asarar da gobarar wacce ta tashi da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis ta janyo musu.

gobara ta janyo asarar dukiya mai yawa a Ogun
Gobara tan janyo asarar dukiya mai tarin yawa a kasuwar katako a Ogun. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Gobarar ta cinye shaguna da dama a kasuwar

Wani da mai suna Tobias Imala da ya shaida faruwar lamarin, ya bayyanawa jaridar The Punch cewa har yanzu ba a iya tantance musabbabin gobarar ba.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Tona Shirin ‘Yan Ta’adda a Lokacin Bukukuwan Sallah a Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Imala ya ƙara da cewa ya hango gobarar ne a lokacin da ya fito ofis da safe, wacce tun a lokacin ta cinye shagunan ajiyar kaya gudu uku, kuma tana ci gaba da ƙara yaɗuwa zuwa wasu shagunan.

Ya kuma ce jama'a sun yi ta ƙoƙarin kawar da kayayyakinsu duk da dai jami'an kashe gobara na jihar Ogun sun kawo ɗauki da wuri.

Wani mai suna Mista Olawale, mai sana'ar siyar da katakai a kasuwar ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne a lokacin da galiban masu shagunan ba su kusa.

Ya bayyana cewa duk da dai gobarar ba ta shafi shagonsa ba, ta cinye aƙalla shaguna 4 da ke maƙwabtaka da nasa.

A kalamansa:

“Yawancin mu ba ma cikin shagunan a lokacin da abin ya faru sakamakon ayyukan ranar muhalli da ke gudana a yau. Gobarar ta tashi ne daga wani shagon siyar da katifa.”

Kara karanta wannan

"Yana Ƙaunata Duk da Banda Hali" Wata Mata Ta Saki Zafafan Hotunanta da Ƙatoton Mijinta

Ma'aikatan kamfanin Indomie sun kawo ɗauki wajen kashe gobarar

Imala ya ƙara da cewa wasu daga cikinsu ne suka garzaya da gudu zuwa kamfanin Indomie, inda ma'aikatan kashe gobara na kamfanin suka zo don kashe gobarar kafin zuwan ma'aikatan kashe gobara na jihar.

Wata ‘yar kasuwa mai suna Deborah Oyeleye, ta ce gobarar ta ƙone duk wasu katakai da ke shagonta, inda ta ce ta yi asarar kayayyakin da kuɗinsu ya kai N400,000.

Wani ɗan guntun bidiyo da aka samu daga wurin da lamarin ya faru, ya nuna yadda ‘yan kasuwa ke rige-rigen kwashe kayayyakinsu a lokacin da gobarar ke ci gaba da laƙume shaguna a kasuwar.

Kwamandan hukumar kashe gobara ta kamfanin Indomin, Bayo Ogundele ya ce gobarar ta cinye aƙalla shaguna 12.

Daliba ta tayar da gobarar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 19

Legit.ng a baya ta kawo muku rahotan wata ɗaliba da ta bankawa makarantar su wuta, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sha tara, waɗanda dukkaninsu mata ne.

Kara karanta wannan

An Bude Iyakar Legas Domin Shigo da Motoci, Gwamnati Ta Yi Watsi da Tsohon Tsari

Wannan mummunan lamari ya auku ne a yankin Guyana da ke Kudancin yankin Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Tags: