"Idan Ba Zaki Girmama Namiji Kada Ki Aure," Mata Budurwa Ta Haddasa Cece Kuce

"Idan Ba Zaki Girmama Namiji Kada Ki Aure," Mata Budurwa Ta Haddasa Cece Kuce

  • Wata 'yar Najeriya da ta shahara kan sharhi kan batutun da suka shafi soyayya ta sake girgiza masu amfani da kafafen sada zumunta
  • Claire Wiyfengla ta shawarci 'yan uwanta mata su yi fatali da zancen cewa namiji da mace duk ɗaya suke idan suna son zaman lafiya a aure
  • A cewar Claire, duk matan da har yanzu suke ganin ɗaya suke da maza, haka zasu kare a gwauraye

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa mai amfani da shafin TikTok ta taɓo matan da su ke tunanin cewa sun kai matsayin da ba zasu yi wa namiji biyayya ko su girmama shi ba.

Claire Wiyfengla ta shaida wa duk macen da take ganin Allah ya tsare ta da yi wa namiji biyayya da ta zauna da kaɗaici ba bu aure.

Wasu matan ba zasu taba aure ba.
"Idan Ba Zaki Girmama Namiji Kada Ki Aure," Mata Budurwa Ta Haddasa Cece Kuce Hoto: TikTok/Clairewiyfengla
Asali: TikTok

Misis Claire ta kara da cewa aure ba na mata masu girman kai bane, waɗanda ke tunanin matsayinsu ɗaya da Namiji a gidan aure.

Kara karanta wannan

"Yana Ƙaunata Duk da Banda Hali" Wata Mata Ta Saki Zafafan Hotunanta da Ƙatoton Mijinta

A ra'ayinta, mace ba zata taɓa zamowa ɗaya da namiji ba musamman idan ana batun aure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aure ba na kowace mace bace, akwai matan da zasu mutu a gwauraye - Claire

Ta kuma ƙara jaddada cewa duk matan da ke tattare da daƙiƙancin cewa ɗaya su ke da maza to ba zasu taɓa yin aure ba a rayuwarsu saboda zaman aure ba na kalarsu bane.

Claire ta rubata a shafinta na TikTok cewa:

"Ba kowace nace bace zata yi aure, idan har kina tunanin ajinki ya wuce ki ƙasa-ƙasa ki wa namiji ladabi da biyayya, idan kina ganin namiji da mace duk ɗaya suke, yar kuwa ki zamanki a gwauruwa."
"Mace ba zata taɓa zama ɗaya da namiji ba har abada."

Kalli bidiyon abinda Claire ta faɗa game da aure

Wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a

Kara karanta wannan

“Kamata Ya Yi Namiji Ya Auri Mace Sama Da 2”: Cewar Wani Mutum, Ya Ba Da Dalilansa

@Tanya ta maida martani da cewa:

"Ni macece, tabbas gaskiya kika faɗa 'yar uwa."

@Tony Max ya ce:

"Muna kira ga gwamnati ta haɗa ki da jami'an tsaron da zasu baki kariya, maganarki dutse ce."

@Freeman ya ce:

"Ke ce mace ɗaya tamkar miliyan kuma ya kamata ki samu cikakkiyar kariya."

"Yana Kaunata Duk da Bani da Hali" Wata Mata Ta Saki Hotunan Mijinta

A wani labarin na daban kuma Wata yar Najeriya mai ilimin kananan halittu ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa Hotunan gabjejen mijinta.

Matar mai suna Sharon ta bayyana cewa jibgegen sahibin na ta yana kaunarta kaunar da babu sirki duk kuwa da wasu halaye mara kyau da rawar kai da take da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262