"Yan Kaunata Duk da Bani da Hali" Wata Mata Ta Saki Hotunan Mijinta
- Wata yar Najeriya mai ilimin kananan halittu ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa Hotunan abokin rayuwarta
- Yayin da ta saki Hotunansu tare, kyakkyawar matar ta ce Mijinta na tsananin kaunarta duk da tana halaye mara kyau
- Mutane da dama sun mata fatan Alheri da kuma taya ta murna amma wasu sun ɗan yi shaguɓe saboda girman da Allah ya ba mijin
Wata mata 'yar Najeriya ma'abociyar son kwalliya da kyale-kyale mai suna Sharon, ta haddasa kace-nace a shafin TikTok bayan ta wallafa hotunan mijinta.
A rubutun da ta wallafa mai haɗe da Hotunan ma'auratan, zankadediyar matar ta yi kalaman yabo kai tsaye ga sahibinta kuma abokin rayuwarta.
Sharon ta bayyana cewa jibgegen sahibin na ta yana kaunarta kaunar da babu sirki duk kuwa da wasu halaye mara kyau da rawar kai da take da su.
Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi
A ɗan gajerin bidiyon an ji Sharon na cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Duk da rawar kaina da rashin ladabi yana so na kuma so na haƙiƙa."
Wannan kalamai na ta ya jawo mutane da dama sun yabe ta, yayin da wasu kuma suka koma tsokanarta.
Wasu kuma sun bai wa kyakkyawat matar shawara ta rufe kunnuwanta karta saurari masu gulma.
Wasu daga cikin martanin mutane ga Sharon
Jenny Bebe ta ce:
"Soyayya ruwan zuma, ina taya ki murna 'yar uwa, ku ci gaba da ƙaunar junanku."
Monday D Dang ya maida martani da cewa:
"Ina taya ki murna 'yar uwa kuma ina rokon Allah ya muku jagora a wannan tarayya, Allah ya muku albarka, Amen."
user9658873358821 ya ce:
"To dama me zai hana ya so ki? Ina taya ki murna yar uwa, Allah ya sa wannan soyayya ta ɗore har abada."
User Olawunmi ya ce:
"To ai ba shi da wani zaɓi da ya wuce ya nuna miki so."
Me Zamu Jira? Magidanci Ya Maida Martani Ga Likitin da Ya Ce Kar Ya Kusanci Matarsa
A wani labarin na daban kuma Wani mutumi ya shiga ƙunci bayan Likita ya shawarce shi da matarsa kar su kusanci juna na tsawon kwanaki 7.
Sai dai mutumin bai ji daɗin wannan shawara ba domin ganinsa wannan jiran bai zama wajibi ba tunda dai an yi musu tsarin iyali.
Asali: Legit.ng