Aminat Yusuf: Gwamnan Legas Ya Bai Wa Dalibar Da Ta Karya Tarihin Shekara 40 Na LASU Kyautar Miliyan 10

Aminat Yusuf: Gwamnan Legas Ya Bai Wa Dalibar Da Ta Karya Tarihin Shekara 40 Na LASU Kyautar Miliyan 10

  • Aminat Yusuf, dalibar lauya a jami’ar jihar Legas (LASU), wacce ta karya tarihin shekaru 40, ta samu kyautar naira miliyan 10
  • Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da kyautar N10m ga Amina a wajen taron da jami’ar ta gabatar
  • Amina ta zama ɗaliba ta farko a LASU da ta samu cikakken CGPA na 5.0 a cikin shekaru 40 da jami’ar ta yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu , ya bai wa Aminat Yusuf, dalibar ɓangaren shari'a a jami'ar jihar Legas (LASU), naira miliyan 10 saboda samun sakamako mafi kyawu, CGPA na 5.0.

Sanwo-Olu ya sanar da bai wa Aminat gudunmawar N5m a karan kansa, da kuma wata N5m daga gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuni, a wajen taron yaye ɗalibai karo na 26 a babbar harabar jami’ar LASU dake Ojo.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Hatsabiban 'Yan Ta'adda 6 Sun Sheƙa Lahira a Arewacin Najeriya

Gwamnan Legas ya bai wa daliba kyautar N10m
Gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu ya bai wa daliba mafi hazaka a LASU kyautar N10m. Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Twitter

Amina ta kafa tarihin da aba taɓa kafawa ba cikin shekaru 40 a jami'ar LASU

Amina ita ce ɗaliba ta farko a LASU da ta sami irin wannan sakamako mai ban mamaki na CGPA 5.0 a cikin shekaru 40.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya wallafa saƙon taya murna da kyautar kuɗaɗen a shafinsa na Tuwita, ranar Alhamis, 22 ga watan Yuni.

Aminat Yusuf, ta janyo hankalin gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, saboda kammala digiri da CGPA 5.0 a fannin shari’a a jami’ar jihar Legas (LASU).

Gwamna Sanwo-Olu, a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuni, ya taya Aminat Yusuf murna kan wannan gagarumar nasara da ta samu.

Channels TV ta ruwaito cewa, jami'ar ta LASU ta kuma bai wa wasu manyan mutane digirin girmamawa a yayin bikin yaye ɗaliban.

Jami’ar Najeriya, LASU ta ɗauki dalibai 10,301 cikin sama da 40,000 da suka nemeta

Kara karanta wannan

Sabon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya Ya Kama Aiki Gadan-Gadan, Ya Ɗauki Manyan Alkawurra

Legit.ng a wani rahoto na baya ta ruwaito cewa, jami'ar jihar Legas (LASU), ta ɗauki ɗalibai 10,301 daga cikin 40,200 da suka nemi shiga makarantar.

Shugaban jami'ar, Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, a wajen bikin yaye ɗaliban makarantar na shekarar 2022/2023 a babbar harabar makarantar da ke Ojo, jihar Legas.

Dubban maniyyata sun maƙale a filin jirgin saman Legas

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa dubban maniyyata aikin hajji ne suka maƙale a filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammed da ke birnin Ikko.

Mafi yawan waɗanda suka maƙala a filin jirgin sun kasance waɗanda suke jiran zuwa aikin hajji ne a jirgin yawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng