Shugaban Sojin Saman Najeriya Ya Kama Aiki, Ya Dauki Babban Alkawari
- Sabon shugaban rundunar sojin saman Najeriya, AVM Hassan Bala Abubakar, ya karbi mulki, ya shiga Ofis a karon farko
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Abubakar a wannan matsayi bayan yi wa baki ɗaya hafsoshin tsaro ritaya
- Da yake jawabin, Abubakar ya lashi takobin ƙara zage dantse domin kawo karshen ayyukan yan ta'adda, 'yan bindiga da sauransu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Sabon hafsan rundunar sojin saman Najeriya, Air Vice Marshal Hassan Bala Abubakar, ya shiga Ofis ya fara aiki a sabon muƙamin da shugaban kasa ya naɗa shi.
Vanguard ta rahoto cewa Oladayo Amao, tsohon shugaban rundunar sojin saman ne ya miƙa wa Abubakar tuta a wani ɗan kwarkwaryar biki da aka shirya a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.
Idan baku manta ba, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa hafsoshin tsaron Najeriya har da sifetan yan sanda na ƙasa ritaya ranar Litinin da ya gabata.
A wata sanarwa da sakataren gwamnati, George Akume, ya sanya wa hannu, Tinubu ya kuma naɗa sabbin shugabannin tsaro, inda aka ga sunan Abubakar a matsayin shugaban sojin sama.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sabon shugaban NAF ya ɗauki muhimmin alkawari
AVM Abubakar ya yi alkawarin ƙara ƙarfafa rundunar sojin sama a ƙoƙarin yaƙi da ta'addaci, ayyukan yan bindiga da sauran kalubalen tsaron da suka addabi ƙasar nan.
Ya kuma sha alwashin cewa zai ci gaba da ƙara yaukaƙa kyakkyawar dangantaka da haɗin guiwar rundunar sojin sama da sauran hukumomin tsaro kamar yadda ya taras, kamar yadda The Cable ta rahoto.
A kalamansa, Abubakar ya ce:
"Tare da haɗin kan abokan aikina zamu ɗora daga abinda muka taras kan umarnin da shugaban ƙasa ya bamu a lokacin zaman majalisar tsaron Najeriya."
"Za kuma mu ƙara kawo sabbin hanyoyi da ɗaukar matakai waɗanda zasu taka rawa wajen kawo karshen kalubalen da muke fama da su kuma su inganta ayyukan dakarunmu."
Sabon IGP Ya Shiga Ofis, Ya Karbi Ragamar Yan Sandan Kasar Daga Hannun Baba
A wani labarin na daban kuma Mukaddashin shugaban hukumar 'yan sandan Najeriya ya shiga Ofi bayan karɓan mulki daga tsohon IGP, Usman Alƙali Baba.
Da yake jawabi, mukaddashin IGP na ƙasa ya bayyana cewa ya fahimci girman nauyin da ke tattare da wannan matsayi da aka naɗa shi.
Asali: Legit.ng