Da Dumi-Dumi: Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Gaskiya Dangane Da Karin Albashi Ga Tinubu Da Shettima

Da Dumi-Dumi: Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Gaskiya Dangane Da Karin Albashi Ga Tinubu Da Shettima

  • Fadar shugaban ƙasa ta musanta batun da ke ta yawo na ƙarin albashin kaso 114% ha ƴan siyasa da ma'aikatan shari'a
  • Hadimin Shugaba Tinubu shine ya musanta hakan a cikin wata sanarwa inda ya bayyana cewa shugaban ƙasar bai amince da ƙarin ba
  • Dele Alake ya bayyana cewa batun ƙarin bai ma iso gaban teburin shugaban ƙasar ba ballantana ya duba yiwuwar amincewa da shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Mai ba Shugaɓa Tinubu shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da tsare-tsare, Dele Alake, ya bayyana cewa shugaban ƙasar bai amince da ƙarin albashi ba ga ƴan siyasa da ma'aikatan ɓangaren shari'a.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Alake ya bayyana cewa duk da cewa aikin hukumar tattara kudaɗen shiga da lura da ƙasafin kuɗi (RMAFC) ne yin duba da ƙara albashin, labaran yin ƙarin a wannan lokacin ƙarya ce tsagwaronta.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shettima Ya Sa Labule da Bill Gates, Ɗangote da Wasu Gwamnoni a Villa, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu bai amince da karin albashi ba ga yan siyasa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: DOlusegun
Asali: Facebook

Dele Alake, ya fitar da sanarwar ne bayan wani furuci da jami'in hukumar RMAFC ya yi na cewa an amince da ƙarin kaso 114% ga ƴan siyasa da ma'aikatan shari'a na ƙasar nan, rahoton The Cable ya tabbtar.

Alake bai musanta cewa hukumar ta RMAFC ta gabatar da shawarar yin wannan ƙarin ba, amma ya bayyana cewa ba za a iya yin ƙarin ba har sai shugaban ƙasa ya amince da hakan, cewar rahoton Premium Times.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaba Tinubu bai amince da ƙarin albashin ba

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Mun lura cike da takaici labarin da ke yawo kan batun ƙarin kaso 114% na albashin shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, zaɓaɓɓun ƴan siyasa da ma'aikatan shari'a."
"Ba tare da wata tantama ba muna sanar da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu, bai amince da wani ƙarin albashi ba, sannan ba a kawo masa wannan shawarar ba ballantana ya duba yiwuwar amincewa da ita."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Cikin Tsakar Dare a Wata Jiha, Rayukan Mutane Da Dama Sun Salwanta

"A yayin da mu ka aminta cewa aikin hukumar RMAFC ne kawo shawara da yanke albashi da alawus na ƴan siyasa da ma'aikata shari'a, hakan ba zai taɓa aiwatuwa ba sai shugaban ƙasa ya yi nazari da amincewa da ƙarin."

Ƴan Najeriya da dama dai sun caccaki batun ƙarin albashin a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke kuka kan ƙarin farashin kayayyaki a dalilin tsare-tsaren gwamnati da suka haɗa da cire tallafin man fetur.

RMAFC Ta Musanta Batun Karin Albashi Ga Tinubu, Shettima, Da Sauransu

A wani labarin kuma, hukumar RMAFC ta fito fili ta musanta labarin ƙarin albashin da aka ce ta yi wa ƴan siyasa da ma'aikatan shari'a na ƙasar nan.

Hukumar ta bayyana har yanzu shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai kai ga amincewa da sabon ƙarin albashin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng