NLC Ta Rufe Hanyar Shiga Kamfanin ’Yan China Saboda Rashin Kulawa Da Kuma Mutuwar Ma’aikaci Dan Najeriya

NLC Ta Rufe Hanyar Shiga Kamfanin ’Yan China Saboda Rashin Kulawa Da Kuma Mutuwar Ma’aikaci Dan Najeriya

  • Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta rufe wani kamfanin 'yan China saboda rashin mutunta ma'aikata
  • Kungiyar ta ce kamfanin ba sa bai wa ma'aikatansu kulawa na abinci da ruwa da magani
  • Rashin kulawar ne ma ta jawo rasa wani daga cikin direbobinsu Mista Augustine rasa ransa saboda rashin magani

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta rufe wani kamfanin 'yan China bisa zargin wulakanta ma'aikanta 'yan Najeriya.

Kamfanin mai suna Shaanxi Construction Engineering Group Corporation ana zarginsa da cin zarafin ma'aikatansa.

NLC ta yi wa kamfanin 'yan China tsinke saboda mutuwar ma'aikaci dan Najeriya
Kungiyar Kwadago Ta Najeriya, NLC. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Kungiyar ta isa harabar kamfanin da ke kusa da sabuwar Hedkwatar ECOWAS a Lugbe da misalin karfe 7:30 na safe.

NLC ta samo tasgaro na shiga harabar kamfanin

Daily Trust ta tattaro cewa da farko an hana kungiyar shiga cikin kamfanin saboda an kulle mashigar, amma daga bisani sun samu damar shiga.

Kara karanta wannan

An Ba Abba Gida-Gida Wa’adin Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano, Cikakken Bayani

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumomin kamfanin ba su ce komai ba kuma ba su mai da martani game da korafe-korafen kungiyar ba.

Gwamnatin kasar China ce ta dauki nauyin gina sabuwar sakatariyar ECOWAS din don kyautata wa mazauna yankin da taimakon su.

Sakataren kungiyar, Emmanuel Ugboaja ya koka kan yadda kamfanin ke wulakanta ma'aikanta akan aiki.

Ya ce ma'iakatan suna aiki ne na wucin gadi ba tare da tsari na harkar lafiya ko walwala ba, Vanguard ta tattaro.

NLC ta bayyana yadda ma'aikacin ya mutu saboda rashin kulawar kamfanin

Ya bayyana yadda wani daga cikin direbibin kamfanin, Mista Augustine ya mutu saboda rashin kulawar gaggawa na magani.

A cewarsa:

"Ba fensho ba giratuti ba abinci ba ruwa kuma babu bayani, ta ina taimako zai fito?
"Kullum muna rokon gwamnati ta samar da yanayi mai kyau amma a banza, wannan shi ne kalubalen da muke fuskanta."

Kara karanta wannan

Rusau: NITP Ta Gargadi Gwamnatin Kano Kan Tsagaita Rushe-rushe, Ta Bayyana Irin Asarar Da Aka Tafka

Kungiyar ta ce za ta ci gaba da kasancewa a harabar kamfanin, yayin da za ta fara tattaunawa da hukumomin kamfanin.

Matar marigayi Mista Augustine ta bayyana cewa kamfanin sun ki su kai shi asibiti kuma suka hana shi komawa gida don neman magani.

NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki, Yayin Da Za Ake Ci Gaba Da Tattaunawa Da Gwamnati

A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi barazanar sake shiga yajin aiki.

Kungiyar ta yi wannan barazanar ne bayan gwamnati ta cire tallafin man fetur a kasar.

Za a ci gaba da tattaunawa yayin da kungiyar ta bukaci a kara mafi karancin albashi saboda yanayin tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.