Mataimakin Shugaban Kasa, Shettima Ya Gana da Jakadan Burtaniya a Najeriya

Mataimakin Shugaban Kasa, Shettima Ya Gana da Jakadan Burtaniya a Najeriya

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya gana da jakadan Burtaniya a Najeriya, Richard Montgomery,a Villa da ke Abuja
  • Mista Montgomery, ya shaida wa yan jarida cewa sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ƙasahen biyu
  • Ya ce Ministoci da yan kasuwa a Burtaniya sun yi na'am da matakan farfaɗo da tattalin arziki da shugaba Tinubu ya fara dauka

FCT Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya gana da jakadan Burtaniya a Najeriya, Richard Montgomery, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Laraba.

Da yake zantawa da yan jaridar gidan gwamnati, Jakadan Burtaniya ya ce ganawarsa da mataimakin shugaban ƙasa ta yi kyau, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Jakadan Burtaniya Ya Gana da Kashim Shettima.
Mataimakin Shugaban Kasa, Shettima Ya Gana da Jakadan Burtaniya a Najeriya Hoto: Kashin Shettima
Asali: Facebook

Muhimman batutuwan da suka tattauna a zaman

Da yake bayyana abinda ya tattauna da Shettima, Jakadan ya ce ganawar ta maida hankali kan yadda za'a ƙara yaukaƙa dangantakar ƙasashem biyu, musamman a bangaren bunƙasa tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mista Montgomery, ya ce Ministocin Burtaniya sun aminta da matakan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ciki harda cire tallafin mai da saita farashin musanyar kuɗi.

Jakadan Burtaniya ya kara da cewa sun tattauna da mataimakin shugaban kasa kan hanyoyin rage wa jama'a raɗafin da zasu shiga musamman sakamakon cire tallafin Fetur.

A kalamansa, Mista Montgomery ya ce:

"Na je Landan makon da ya gabata kuma na yi wa Ministocinmu bayani, sannan na tattauna da yan kasuwa a ɓangaren hada-hadar kuɗi, banki da zuba hannun jari kuma sun faɗi kalamai masu daɗi kan matakan da Najeriya ke ɗauka."
"Mun san cewa wannam lokaci ne mai wahala duba da tashin farashin kaya da rashin ayyukan yi. Ni da mataimakin shugaban ƙasa mun lalubo wasu hanyoyi da mai yuwuwa zasu rage wa mutane matsin da suka shiga."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sallami Hafsoshin Tsaro da IGP Daga Aiki, Ya Naɗa Sabbin Da Zasu Maye Gurbinsu

Montgomery ya nuna kwarin guiwar cewa matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka ka iya sauya akalar ƙasar nan zuwa hanyar farfaɗowa da bunƙasa, kamar yadda Guardian ta rahoto.

Sabon IGP Ya Shiga Ofis, Ya Karbi Ragamar Yan Sandan Kasar Daga Hannun Baba

A wani rahoton na daban kuma Sabon mukaddashin shugaban yan sandan Najeriya ya kama aiki bayan naɗin da shugaba Tinubu ya masa.

Tsohon Sifetan 'yan sanda na ƙasa, Usman Alkali Baba, ne ya miƙa masa ragama a hedkwatar hukumar da ke Abuja ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262