Bene Ya Ruguje Tare Da Kashe Yaro Dan Shekara 15, Gwamnati Ta So Rushe Benen Kafin Yanzu
- Wani bene ya ruguje akan wani yaro dan shekara 15 tare da kashe shi nan take akan hanyar Shiroro da ke Minna cikin jihar Niger
- Marigayin mai suna Sallah an tabbatar da cewa dan makarantar Islamiyya ne, yana zaune da abokansa ne lokacin da abin ya faru
- An tabbatar cewa Hukumar Raya Birane ta jihar Niger ta dade da saka jan layi a gidan saman don rusa shi tun kafin faruwar lamarin
Jihar Neja - Wani gidan sama ya rushe tare da kashe wani yaro dan shekara 15 mai suna Sallah akan hanyar Shiroro da ke Minna babban birnin jihar Niger.
Sallah wanda dalibin makarantar Islamiyya ne ya rasu lokacin da suke zaune a jikin gidan saman suna hutawa da abokansa.
Daily Trust ta tattaro cewa matakalar gidan saman ne ta fado akan yaron inda ya mutu nan take sauran abokansa kuma suka samu raunuka.
Wani mazaunin yankin ya bayyana yadda benen ya fado kan yaron
Wani daga cikin mazauna yankin ya tabbatar da cewa ginin ba a kammala shi ba fiye da shekara kuma ba a yi aiki mai inganci ba yayin ginin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
"Mun dade muna kokawa akan ingancin ginin, yaron da ya rasu har da safe muna tare da shi.
"Ya ce mana zai siyo katin waya don ya kira mahaifiyarsa a kauye, ya kasance makocinmu ne.
"Yana zaune da abokansa lokacin da matakalar gidan saman ta fado kansa inda ya mutu nan take.
Hukumar Raya Birane tun a baya ta so rushe ginin kafin faruwar hakan
Hukumar Raya Birane ta jihar Niger ta dade da saka alamun rushe wannan gidan saman kafin ya rushe, cewar rahotanni.
Kokarin samun wanda ya mallaki gidan saman ya ci tura inda aka tabbatar da cewa yana babban birnin Tarayya Abuja.
Bene Mai Hawa 7 Ya Ruguje Tare Da Danne Ma'aikata a Jihar Legas
A wani labarin, wani dogon gini mai hawa bakwai ya ruguje tare da danne ma'aikata a jihar Lagos.
Ginin ya fadi ne a unguwar Banana Island da ke jihar inda mutane da dama suka makale a ciki.
Masu ba da agajin gaggawa sun isa wurin don ganin sun zagulo mutanen da suka makalen.
Asali: Legit.ng