'Yan Sanda Sun Kama Ma'aikatan Jinya 2 Da Mai Gadin Asibiti Bisa Zargin Satar Mabiyiya, Sun Ce Kare Ya Cinye

'Yan Sanda Sun Kama Ma'aikatan Jinya 2 Da Mai Gadin Asibiti Bisa Zargin Satar Mabiyiya, Sun Ce Kare Ya Cinye

  • Jami'an 'yan sandan jihar Ondo sun kama wasu mutane uku da ake zargi da satar mabiyiya a asibiti bayan haihuwar jaririya
  • Mutanen uku, wadanda suka hada da ma'aikatan jinya biyu da wani mai gadi guda daya an kama su ne a wata cibiyar lafiya da ke Owo a jihar
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce mutanen uku na hannunsu

Jihar Ondo - Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta cafke ma'aikatan jinya guda biyu da wani mai gadi bisa zargin sace mabiyiyar matar da ta haihu.

Wadanda ake zargin suna aiki ne a cibiyar lafiya ta Comprehensive a Emure Ile, Owo da ke cikin jihar Ondo.

'Yan sanda sun kama ma'aikatan lafiya 2 da mai gadin asibiti bisa zargin satar mabiyiya a Ondo
Kakakin 'Yan Sandan Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya. Hoto: Peoples Gazette.
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa an zarge su da sace mabiyiya bayan haihuwar jarirya bayan iyayen yarinyar sun kai rahoton zuwa ofishin 'yan sanda.

Kara karanta wannan

NAHCON Ta Ce Maniyyata 6,000 Ne Kadai Ba A Yi Jigilarsu Zuwa Saudiyya Ba, Ta Bayyana Dalilai

Mahaifin jaririyar ya ce asibitin sun ki bai wa matarsa mabiyiyar

Mahaifin jaririyar, Tunde Ijanusi ya ce asibitin sun ki su bai wa matarsa mai suna Joy mabiyiya bayan ta haihu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ijanusi ya bayyana cewa duk kokarin da ya yi don samun mabiyiyar daga ma'aikatan asibitin ya ci tura.

Daya daga cikin kakannin jaririyar ta ce lokacin da ta samu likitocin akan mabiyiyar sai suka ce mata ai kare ne ya shiga asibitin ya cinye mabiyiyar.

Ta kara da cewa daga cikin ma'aikatan asibitin ya bukaci da su manta da abin don kada jama'a su san me ake ciki.

Yayin da tace ba su yi wata-wata ba suka kai rahoton ofishin 'yan sanda don daukar mataki na gaggawa, cewar Tribune.

Rundunar 'yan sandan jihar sun tabbatar da kama mutanen uku

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wata Mata Manajar Banki, Sun Dade Suna Yi Mata Gargadi

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce dukkan mutane ukun da ake zargi suna komarsu.

A cewarta:

"Muna kan binciken wadanda ake zargin su uku, kuma zamu binciko tushen abin don daukar mataki."

Malamin Addinin Da Aka Sace a Jihar Ondo Ya Kubuta Daga Hannun Masu Garkuwa

A wani labarin, Malamin addinin Musulunci da aka sace, Ibrahim Oyinlade a jihar Ondo ya kubuta.

Malamin mai shekaru 67 a duniya an sace shi ne a gonarsa a ranar Asabar 17 ga watan Yuni.

Dan uwan malamin wanda bai so a ambaci sunansa ba ya tabbatar da cewa an sako malamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.