Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Binciki Cirar N370 Da Ake a Albashin Ma'aikata Da 'Yan Fansho

Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Binciki Cirar N370 Da Ake a Albashin Ma'aikata Da 'Yan Fansho

  • Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da cire N370 daga albashin kowane ma'aikaci da ƴan fanshon da ake yi a jihar
  • Gwamnatin ta kuma bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano dalilin cirar kuɗin wanda yake ba bisa ƙa'ida
  • An tattaro cewa kuɗaɗen dai ana tura su ne zuwa asusun wani kamfani mai suna Share Benefit Investment Limited

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da cire N370 daga cikin albashin albashin ma'aikata da ƴan fansho a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Abdullaji Baffa Bichi shi ne ya bayyana hakan a cikin wata wasiƙa da ya aike zuwa ga shugabannin hukumomin gwamnatin jihar, cewar rahoton Daily Trust.

Gwamnatin Kano ta dakatar da cirar N370 daga albashin ma'aikata
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Thesun.com
Asali: UGC

Sakataren gwamnatin jihar ya bayyana cewa an dakatar da cire kudin nan ta ke har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan yadda aka yi aka assasa cirar kuɗin.

Kara karanta wannan

Rusau A Kano: Mun Kwato Filayen Tiriliyoyin Nairori, Gwamnatin Kano Ta Yi Karin Bayani

An tattaro cewa gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ita ce ta kawo tsarin cirar kuɗin sannan duk kuɗaɗen da aka cira ana tura su ne zuwa asusun wani kamfani mai suna Share Benefit Investment Limited.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnatin za ta gudanar da bincike kan lamarin

Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:

"Gwamnatin jiha ta lura cikin takaici da cirar N370 ba bisa ƙa'ida ba daga albashin kowane ma'aikaci da ƴan fansho a jihar nan, sannan daga baya a tura zuwa asusun kamfanin Share Benefit Investment Limited."
"A dalilin hakan mai girma gwamnan jihar Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin dakatar da cirar kuɗin nan ta ke da kuma tura su zuwa asusun kamfanin har sai zuwa lokacin da za a kammala bincike kan wannan cirar kuɗin wanda bai dace ba."

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Matar Da Ta Farfado Ana Shirin Kaita Makwanci Ta Sheka Da Gaske

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin bincikar gwamnatin magabacinsa inda ya fara da rushe gine-ginen da aka yi akan filayen gwamnati waɗanda gwamnatin baya ta rabar.

An Ba Abba Gida-Gida Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano

A wani labarin kuma, wata ƙungiya ta yo kan Abba Gida-Gida dangane da rushe-rushen da yake a jihar Kano wanda a cewarta hakan ba shugabanci bane mai kyau.

Kungiyar Good Governance and Change Initiative (GGCI) ta ba gwamnan wa'adin sa'o'i 24 da ya dakata ko kuma ta maka shi ƙara a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng