Shugaba Tinubu Ya Mayar Da Wasu Hukumomi 2 a Karkashin Ofishin Kashim Shettima

Shugaba Tinubu Ya Mayar Da Wasu Hukumomi 2 a Karkashin Ofishin Kashim Shettima

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar da hukumomin bayar da agajin gaggawa ta ƙasa da hukumar Alhazai zuwa ofishin mataimakin shugaban ƙasa
  • Matakin mayar da hukumomin NEMA da NAHCON a ƙarƙashin Kashim Shettima yana bisa kan tanadin dokar kafa su
  • Shugaban ƙasa Tinubu ya kuma amince da sake fasalin ofishin na mataimakin shugaban ƙasa

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin wasu hukumomi guda biyu su koma aiki a ƙarƙashin ofishin mataimakinsa, Kashim Shettima domin bin umarnin tanadin dokar kafa su.

Hakan ya bayyana ne a cikin wata sanarwa da hukumar talbijin ta ƙasa (NTA) ta yi a shafinta na Twitter a yammacin ranar Talata, 20 ga watan Yunin 2023.

Shugaba Tinubu ya mayar da wasu hukumomi biyu ofishin Kashim
Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Jerin hukumomin da shugaba Tinubu ya mayar a ƙarƙashin ofishin Kashim Shettima

Kara karanta wannan

Ayyukan Femi Gbajabiamila 8 A Matsayinsa Na Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tinubu

Hukumonin da lamarin ya shafa sun haɗa da hukumar jindaɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) da hukumar bayar da agaji da kiyaye iftila'i ta ƙasa (NEMA).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sanarwar kuma, Shugaba Tinubu ya kuma amince da sauya fasalin ofishin mataimakin shugaban ƙasar ciki har da ƙarin hadimai waɗanda za su yi aiki tare da mataimakin shugaban ƙasar domin gudanar da ayyukansa yadda suka dace.

Wannan dai na daga cikin sauye-sauyen da shugaban ƙasar ya duƙufa kawo wa ne tun bayan ɗarewarsa kan mulki.

Abinda Sugaba Tinubu ya yi tun bayan zamansa shugaban ƙasa

Tun bayan da ya shugaban ƙasar Najeriya, Shugaba Tinubu ya duƙufa kawo sauye-sauye domin dawo da ƙasar nan akan turba, waɗanda masu sharhi da dama sun yaba masa akai.

Wasu daga cikin sauye-sauyen da ya kawo a cikin satinsa uku akan mulki sun haɗa da cire tallafin man fetur, rattaɓa hannu kan dokar ba ɗalibai bashi da sauransu.

Kara karanta wannan

Daga Rantsar Da Shi Sabon IGP Ya Aike Da Muhimmin Gargadi Ga Miyagu Da Makiyan Najeriya

Tinubu Ya Shilla Kasar France

Rahoto ya zo cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shilla zuwa ƙasar France domin halartar wani muhimmin taro na tattalin arziƙi a ƙasar.

Wannan dai shine karon farko da Shugaba Tinubu ya shilla zuwa ƙasar wajen tun bayan da ya hau kan madafun ikon shugabancin ƙasar nan a ƙarshen watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng