Kotu Ta Kara Tura Sheikh Idris Abdul'aziz Gidan Yari Tsawon Wata Guda
- Kotun Musulunci ta umarci a tsare Dakta Idris Dutsen Tanshi a gidan gyaran hali na tsawon wata guda
- A zaman ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, mai shari'a Turaki, ya yanke wannan hukunci bisa zargin malamin ya raina Kotu
- Ma'aikatan shari'a ta jihar Bauchi ce ta shigar ƙarar Sheikh Idris, kuma sai da aka yi zaman Kotu biyu duk bai halarta ba
Bauchi - Babbar Kotun Musulunci mai zama a jihar Bauchi, ta sake tura fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dakta Idris Abdul’aziz, gidan yari tsawon wata ɗaya.
Rahoton Aminiya ya nuna cewa Kotun ta sake bada umarnin tsare babban limamin Masallacin Dutsen Tanshi a kurkuku ne bisa zargin ya, "Raina kotu."
Alkalin Kotun, mai shari'a Malam Hussaini Turaki, ne ya yanke wannan hukuncin yayin zaman sauraron ƙarar ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023.
Hukuncin alkalin na nufin Sheikh Idris Abdul'aziz, zai ci gaba da zama a Kurkuku har zuwa ranar 19 ga watan Yuli, 2023 lokacin da za'a dawo domin ci gaba da sauraron ƙarar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abinda ya sa Alkalin ya yi zargin Malamin ya raina Kotu
Tun da fari, ma'aikatar shari'a a jihar Bauchi ta maka Malamin a gaban Kotun shari'ar Musulunci kuma bayanai sun nuna an tura masa da takardar sammaci.
Sai dai a ranar 31 ga watan Mayu, 2023 da Kotu ta zaɓa domin fara zaman shari'a, Dakta Idris bai halarta ba, amma lauyiyinsa suka gabatar da uzurin cewa ba shi da lafiya.
Daga nan ne mai shari'a Turaki ya umarci dakarun 'yan sanda su kamo Malamin duk inda suka ganshi sakamakon ƙin zuwa zaman Kotu kamar yadda aka shaida masa a takardar sammaci.
Alkalin ya ɗage zaman zuwa ranar 5 ga watan Yuli, nan ma aka dawo amma Dakta Idris bai zo ba a karo na biyu, lauyoyinsa suka sake faɗa wa Kotu ba shi da lafiya.
Lauyoyin Malamin sun kuma shigar da buƙatar Kotu ta janye umarnin da ta bai wa jami'an tsaro a baya na kamo Sheikh Idris. Alkalin ya ɗage zama zuwa 19 ga watan Yuni don yanke hukunci kan buƙatar.
Gwamnatin Bauchi ya tuhumar Malam Idris Dutsen Tanshi da yin kalaman da ka iya tada zaune tsaye da rashin ɗa'a ga Manzon Allah (SAW).
EFCC Ta Titsiye Tsohon Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom
A wani labarin na daban kuma Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Benuwai kuma jigon PDP, Samuel Ortom, ranar Talatan nan.
EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa, ta gayyaci tsohon gwamnan ne domin amsa wasu tambayoyi.
Asali: Legit.ng