Rusau: NITP Ta Gargadi Gwamnatin Kano Kan Tsagaita Rushe-rushe, Ta Bayyana Irin Asarar Da Aka Tafka

Rusau: NITP Ta Gargadi Gwamnatin Kano Kan Tsagaita Rushe-rushe, Ta Bayyana Irin Asarar Da Aka Tafka

  • Wata kungiya a Najeriya ta gargadi gwamnatin jihar Kano ta tabbatar ta tsagaita rushe-rushen da take yi don ganin an nemo hanyar da ta dace
  • Kungiyar Masu Tsara Birane (NITP) ita ta yi wannan gargadi ta bakin shugabanta, Nathaniel Atebije a ranar Litinin 19 ga watan Yuni a Abuja
  • Kungiyar ta ce rushe-rushen yana matukar shafar mutane musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki a kasar

Jihar Kano - Kungiyar Masu Tsare Birane a Najeriya (NITP) ta gargadi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir da ya tsagaita rushe-rushen da yake yi.

Gwamnatin jihar dai ta dukufa wurin rushe-rushen wuraren da take ganin an siyar tare da gina su ba tare da bin ka'ida ba, wanda ya jawo asarar fiye da N120bn.

NITP ta gargadi gwamnatin jihar Kano kan rushe-rushe a jihar
NITP Ta Gargadi Abba Kabir Yusuf Kan Rushe-rushe. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Nathaniel ya gargadi Abba Gida Gida kan rusau a jihar Kano

Kara karanta wannan

Rusau: Abba Kabir Ya Ce Ba Za Su Yi Asara Ba, Zai Yi Amfani Da Burbushin Rushe-rushen Don Gyara Ganuwoyin Kano

Shugaban kungiyar, Nathaniel Atebije shi ya bayyana haka a ranar Litinin 19 ga watan Yuni a Abuja, inda ya ce gargadin ya zama dole duba da yadda mutane ke korafi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ko da kuwa abin ya dace, dole a rinka sara ana duba bakin gatari bayan dogon bincike da kungiyar ta yi akan rusau din, cewar Daily Trust.

A cewarsa:

"A lissafinmu na karshe an yi asarar fiye da N120bn a yadda ake cikin matsin tattalin arziki a kasar."

Ya ce gwamnatin ya kamata ta yi Rusau din cikin tsari da kwarewa

Kamar yadda The Guardian ta tattaro Nathaniel ya kara da cewa:

"Muna kira ga gwamnati da ta tsagaita rushe-rushen nan, ta yi shi cikin kwarewa ba tare da an musgunawa mutane ba.
"Dimokradiyya 'yar tattaunawa ce da kuma hadin kai, wannan abu yana shafar mutane sosai musamman a wannan yanayi na matsin tattalin arziki."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An yi ram da wasu mazauna Qatar, rikakkun 'yan safarar kwaya a wata jiha

Gwamnatin Kano Ta Biyawa Dalibai 55,000 Kudin Jarrabawar NECO Don Inganta Ilimi

A wani labarin, gwamnatin jihar Kano ta amince da biyan kudaden jarabawar NECO ga dalibai 55,000.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf shi ya amince da biyan kudaden don ganin ilimi ya inganta a jihar baki daya.

Gwamnan ya roki daliban da suka ci gajiyar tallafin da su dage don samun sakamako mai kyau da iyayensu har ma da gwamnati za su yi alfahari da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.