Abubuwan da Ya Dace Kowa Ya Sani Kan Sababbin Shugabannin Soji, IGP da Kwatsam
- Bola Ahmed Tinubu ya yi wa duka hafsohin tsaro masu-ci ritaya, ya nada wadanda za su gaje su
- A sanarwar da aka fitar daga ofishin SGF, an ji an samu hafsoshin sojoji da wasu manyan jami’an tsaro
- Mai girma shugaban kasa ya nada sababbin Shugabanni ga hukumar kwastam da rundunar ‘yan Sanda
A ranar Talata, The Cable ta kawo bayani a game da sababbin hafsoshin tsaron da aka nada:
1. Manjo Janar C.G Musa ya gaji Irabor
A ranar Kirismetin 1967 aka haifi C.G Musa a garin Sokoto, said ai iyayensa mutanen Zangon Kataf ne a garin Kaduna, bayan ya girma ya shiga NDA.
Manjo Janar C.G Musa ya rike shugabancin Operation Hadin Kai a shekarar 2021, ya jagoranci yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso gabas.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2. COAS: Taoreed Lagbaja ya shiga tarihi
Abiodun Lagbaja, Manjo Janar ne da aka haifa a kauyen Ilobu da ke Irepodun a Osun a 1968. Jaridar ta ce ya karanci ilmin wurare, a 1992 ya zama Laftanan.
Lagbaja ya na da digirgir daga makarantar koyon yaki ta Amurka kuma ya rike GOC a Kaduna. Rabon da Bayarabe ya zama COAS tun Alani Akinrinade a 1980.
3. Emmanuel Ikechukwu Ogalla ya zama CNS
Shi ma Emmanuel Ikechukwu Ogalla an haife shi ne a 1968 a Igbo Eze a Enugu. A 1987 ya samu A1 a kowane darasi illa Ingilishi a jarabbawar WASC a NMS.
Haka zalika shi ma ya zama soja ne a shekarar 1992, ya kai matsayin rear admiral bayan kusan shekaru 20. Ogalla ya taba zama Darektan bincike na sojojin ruwa.
4. HB Abubakar zai shugabanci sojojin sama
A garin Shanono a Kano aka haifi Hassan Bala Abubakar a Satumban 1970. Sabon hafsun ya na cikin wadanda su ka zama sojojin saman Najeriya a Satumban 1992.
Air Wice Marshal HB Abubakar ya rike mukamai da-dama a gidan soja kafin wannan mukami.
5. Emmanuel Undiandeye
Emmanuel Undiandey mutumin Obudu ne a Kuros Ribas. Kwararren soja ne da ya yi aiki har da majalisar dinkin Duniya, kafin zamansa DMI, ya yi aiki a sashen a 2020.
6. Bashir Adewale Adeniyi
Bashir Adewale Adeniyi ya zama shugaban Kwastam, an fi saninsa da Kakakin hukumar. Shi ne jami’in da ya gano $8.07m da za a fita da shi ta filin jirgi a Legas.
Saboda gaskiyar da ya nuna a filin jirgin Murtala Muhammed, aka ba shi lambar MFR.
7. Sabon IGP: Kayode Egbetokun
Kamar yadda aka ji labari, a 1990 Kayode Egbetokun ya fara aikin ‘dan sanda. Ana haka har ya kai matsayin Sufritanda, ya zama babban jami’in tsaron Bola Tinubu.
A lokacin da Tinubu yake gwamna, sabon Sufetan ‘Yan sandan ne ya rike masa CSO. Egbetokun ya yi digirinsa ne a lissafi da kuma digirgir da MBA duk a jihar Legas.
Asali: Legit.ng