FG Ta Koma Teburin Tattauna da NLC, TUC Kan Cire Tallafin Man Fetur

FG Ta Koma Teburin Tattauna da NLC, TUC Kan Cire Tallafin Man Fetur

  • Gwamnatin shugaba Tinubu ta sake komawa teburin tattaunawa da wakilan kungiyoyin kwadugo kan batun cire tallafin man fetur
  • Wannan taro zai tattauna kan lalubo hanyoyin da gwamnati zata bi domin saukaka wa yan Najeriya radaɗin cire tallafi
  • Manyan jiga-jigan gwamnati ciki harda sabbin masu ba da shawara da Tinubu ya naɗa kwanan nan sun halarci taron yau Litinin

FCT Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya ta koma teburin tattaunawa da ƙungiyoyin kwadugo NUC da TUC da nufin lalubo hanyoyin rage raɗaɗin cire tallafin mai ga 'yan Najeriya.

The Cable ta tattaro cewa a ranar 5 ga watan Yuni, ƙungiyoyin suka janye shirinsu na shiga yajin aiki da nufin nuna adawa da zare tallafin Fetur bayan sun gana da wakilan FG.

FG Ta ci gaba da ganawa da NLC, TUC.
FG Ta Koma Teburin Tattauna da NLC, TUC Kan Cire Tallafin Man Fetur Hoto: thecable
Asali: UGC

Taron yau Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023 ya gudana a ɗakin taro na ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, da ke cikin Villa a Abuja.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Man Fetur: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki Idan Gwamnatin Tarayya Ta Yi Abu 1

Jerin waɗanda suka halarci taron daga ɓangaren NLC da TUC

Waɗanda suka halarci taron sun ƙunshi shugaban ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, shugaban ƙungiyar 'yan kasuwa (TUC), Festus Osifo, da sauran wakilan 'yan kwadugo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wakilin FG da suka halarci taron yau Litinin

A bangaren gwamnatin tarayya, waɗanda aka hanga sun halarci taron sun haɗa da, mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake, da shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari.

Sauran mahalarta taron sun ƙunshi mai ba da shawara kan tattara haraji, Zacch Adedeji, mai ba shawara kan harkokin wutar lantarki, Olu Verheijen, babban Sakataren ma'aikata ƙwadugo da samar da aiki, Gbenga Komolafe, da sauransu.

Rahoto Channels tv ya nuna cewa ana tsammanin sakamakon zaman da abubuwan da aka cimmawa yayin wannan taro zai biyo baya nan gab kaɗan.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Asri Dakubo Ya Tona Asirin Wasu Sojoji Da Ke Ɗaukar Nauyin Ɓarayin Mai a Najeriya

Idan baku manta ba Kotun ɗa'ar ma'aikata ta haramtawa ƙungiyoyin kwadugo shiga yajin aiki kan batun cire tallafin man Fetur da FG ta yi.

Dalilin da Ya Sa Na Marawa Akpabio Baya Har Ya Zama Shugaban Majalisa, Wike

A wani labarin na daban kuma Nyesom Wike, babban jigon PDP ya bayyana maƙasudin mara wa Akpabio baya har ya zama shugaban majalisar dattawa.

Wike ya bayyana cewa ya mara wa Sanata Akpabio baya har ya zama shugaban majalisar dattawa ne saboda alherin da ya masa a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262