Shugaba Tinubu Ya Nada Sababbin Masu Bada Shawara 5 Daf da Zai Bar Najeriya
- Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya nada wasu karin mutanen da za su rika ba shi shawara a mulki
- A cikin wadanda aka ba mukaman nan akwai Hadiza Bala Usman da Hannatu Musa Musawa
- Bola Tinubu ya nada masu ba shi shawara a kan harkokin majalisa, sannan ya tabbatar da NSA
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin karin wasu da za su zama cikin masu ba shi shawara wajen gudanar da mulkinsa.
Labari ya zo daga The Cable cewa Mai girma shugaban kasa ya zabi Hadiza Bala Usman a matsayin mai bada shawara a wajen kula da tsare-tsare.
Hannatu Musa Musawa ta zama mai ba shugaban Najeriya shawara a harkar al’adu da nishadi.
Mata 2 sun zama Hadimai
Kafin zaman ta mai bada shawara, Hadiza Bala Usman ta rike shugabancin hukumar NPA da shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnatin Kaduna.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Legit.ng Hausa ta fahimci Hannatu Musa Musawa ta na cikin wadanda su ka taka rawar gani wajen yakin neman zaben Bola Tinubu a APC mai-ci.
Mahaifinta, Musa Musawa kwararren ‘dan siyasa ne da aka yi a Katsina a lokacin tsohuwar Kaduna. Ita kuma Lauya ce da tayi karatu a gida da waje.
Masu bada shawara a Majalisa
Rahoton tashar Channels ya ce Sanata Abdullahi Abubakar Gumel ya zama babban mai bada shawara na musamman a kan harkar majalisar dattawa.
A gefe guda kuma tsohon ‘dan majalisa, Hon. (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim zai rika ba shugaban Najeriya shawara a kan harkokin majalisar wakilai.
Sauran mukamai da aka bada
Haka zalika Mallam Nuhu Ribadu ya samu karin matsayi daga mai bada shawara na musamman a kan tsaro zuwa NSA, ya shiga majalisar tsaro ta kasa.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya ce Adeniyi Bashir Adewale ya zama sabon shugaban kwastam, ya na mai canzar Kanal Hameed Ali.
Sababbin Hadiman shugaban kasa
1. Hadiza Bala Usman
2. Hannatu Musa Musawa
3. Sanata Abdullahi Abubakar Gumel
4. Hon. (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim
5. Mallam Nuhu Ribadu
Hafsoshin tsaro sun tafi
A jiya rahoto ya zo cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sababbin shugabannin hukumomin tsaron Najeriya, an yi wa duka hafsoshin tsaro ritaya.
Bola Tinubu ya amince da naɗin CDS, COAS, IGP, NSA a yammacin Litinin 19 ga watan Yuni. Sanarwar ta fito ne a lokacin da yake shirin tafiya Faransa.
Asali: Legit.ng