Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an INEC, Sun Yi Awon Gaba da Matarsa a Ebonyi

Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an INEC, Sun Yi Awon Gaba da Matarsa a Ebonyi

  • Wasu miyagun 'yan bindiga da ba'a sani ba sun kashe ma'aikacin hukumar INEC a jihar Ebonyi ranar Lahadin da ta shige
  • Rahoto ya nuna sun kashe mutumin, Emmanuel Igwe, a hanyarsa ta komawa gida daga jihar Abiya kuƙa sun yi awon gaba da matarsa
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar ya ce tuni jami'ai suka fara farautar makasan kuma suna fatan zasj shigo hannu nan ba da jimawa ba

Ebonyi - Wasu tsagerun 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun harbe ma'aikacin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) har lahira a jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ma'aikacin INEC ɗin, Emmanuel Igwe, ya gamu da ajalinsa a hannun yan bindigan a yankin ƙaramar hukumar Ivo, jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Ajalinsu Yayin da Suka Kai Hari Sansanin Jami'an Tsaro, Da Dama Sun Mutu

Harin yan bindiga a jihar Ebonyi.
Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an INEC, Sun Yi Awon Gaba da Matarsa a Ebonyi Hoto: vanguard
Asali: Twitter

Mamacin, wanda ya kai matsayin mataimakin shugaban INEC na ƙaramar hukumar Afikpo, ya gamu da yan ta'addan yayin da yake hanyar komawa gida daga jihar Abiya.

Haka zalika rahoto ya nuna cewa matar mutumin, wacce har yanzu ba'a bayyana sunanta ba, tana hannun 'yan bindigan sun yi garkuwa da ita.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar The Nation ta rahoto cewa kwamishinar hukumar zaɓe reshen jihar Ebonyi, ta tabbatar da kashe ma'aikacinta da kuma garkuwa da mai ɗakinsa.

Ta ce:

"Yan bindiga sun harbi ɗaya daga cikin abokan aikinmu, mataimakin shugaban zaɓe na ƙaramar hukumar Afikpo, Emmanuel Igwe, har lahira a yankin IVo, yana hanyar dawowa daga Abiya kuma sun tafi da matarsa."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka kan lamarin?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Ebonyi, SP Onome Onovwakpoyeya, ya tabbatar faruwar lamarin. Ya ce maharan sun harbi mutumin ta gilashin motarsa ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Babban Jigon da Alamu Suka Nuna Zai Koma APC, Ya Roƙe Shi Alfarma 1

Kakakin 'yan sandan ya ce:

"Mun fara aikin farautar waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki kuma muna fatan nan ba da jimawa ba zasu shigo hannu. Sun harbi mamacin ta gilashin ƙofa kuma abun ya zo da ƙarar kwana."

Yan Bindiga Sun Sheka Barzahu Yayin da Suka Kai Wa Jami'an Tsaro Hari

A wani labarin kuma kun ji cewa Wasu 'yan bindiga 15 sun kwashi kashinsu a hannun dakarun 'yan banga a yankin ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Rahoto ya nuna cewa 'yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan bangan da tunanin suna bacci da safiyar Litinin, 19 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262