'Yan Bindiga Sun Harbe Wani Da Ya Yi Niyyar Tserewa Daga Komarsu, Matashin Ya Tsira Da Raunuka A Kaduna
- Wasu 'yan bingiga a jihar Kaduna sun harbi wani matashi mai suna Ifeanyi bayan ya yi kokarin tserewa daga hannunsu a dajin karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna
- Wanda abin ya shafa ya samu damar tserewa duk da harbin da ke kafarsa yayin da wasu manoma da ke aiki a cikin gonarsu suka kira 'yan sa kai don daukarshi zuwa asibiti
- Wani mazaunin garin Kagarko, Shu'aibu Bala ya tabbatar da cewa tabbas an harbi kafar Ifeanyi bayan ya yi kokarin guduwa, amma duk da haka ya tsira daga hannunsu
Jihar Kaduna - 'Yan bindiga sun harbe kafar wani da ya yi kokarin tserewa daga hannun su a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
An bayyana sunan wanda aka harban mai suna Ifeanyi bayan ya yi kokarin tserewa a cikin dajin Kagarko da ke jihar.
Daily Trust ta tattaro cewa Ifeanyi wanda ke da babban kanti na siyar da kaya an sace shi ne a ranar Laraba 14 ga watan Yuni da dare a cikin garin Kagarko.
Yadda matashin ya yi niyyar tserewa daga 'yan bindigan
Da yake tabbatar da harbin, wani mazaunin yankin, Shu'aibu Bala ya ce an harbi kafar Ifeanyi ne yayin tserewa a dajin a ranar Juma'a 16 ga watan Yuni.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce wanda abin ya shafa ya samu kwarin gwuiwar guduwa duk da harbin da ke kafarsa kafin wasu manoma suka kira 'yan sa kai aka wuce da shi asibiti don samun kulawa.
Kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar akan faruwar lamarin ya ci tura saboda rashin samun wayarsu.
Gwamna Uba Sani ya sha alwashin kawo karshen 'yan bindiga a Kaduna
Yankin Arewacin Najeriya dai na fama da hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane musamman Arewa maso Yamma.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya sha bayyana aniyarsa na kawo karshen masu garkuwa da mutane da kuma 'yan fashin daji a jihar baki daya.
Tsagera Sun Halaka Manoma Da Dama a Jihar Kaduna
A wani labarin, 'yan bindiga sun hallaka wasu manoma da dama a wani harin da suka kai a jihar Kaduna.
Harin ya afku ne a kauyen Dogon Dawa da ke karamar hukumar Birnin Gwari cikin jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da rana a ranar Asabar 17 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng