Abba Bai Zo Da Wasa Ba: Gwamnatin Kano Ta Biyawa Dalibai 55,000 Kudin Jarrabawar NECO Don Inganta Ilimi

Abba Bai Zo Da Wasa Ba: Gwamnatin Kano Ta Biyawa Dalibai 55,000 Kudin Jarrabawar NECO Don Inganta Ilimi

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir da aka fi sani Abba Gida Gida ya amince da biyan kudin jarrabawar dalibai da suke matakin karshe a makarantun sakandare su 55,000
  • Gwamnan ya ce ya biya kudin wannan jarrabawar da Hukumar Jarrabawar NECO ke shiryawa 'yan makarantun sakandare don inganta harkar ilimi a jihar
  • Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da sakataren yada labaransa, Sanusi Bature ya fitar a ranar Lahadi 18 ga watan Yuni inda roki daliban su dage sosai

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan kudin jarrabawar dalibai 55,000 da za su rubuta jarrabawar karshe a makarantun sakandare wanda Hukumar Shirya Jarrabawa ta (NECO) ke shiryawa.

Gwamnan ya ce wannan na daga tsare-tsarensa don tabbatar da inganta harkar ilimi da kuma ba ta kulawar da ta dace.

Kara karanta wannan

Tsadar Man Fetur: Gwamnan Arewa Ya Samo Mafita, Za a Fara Jigilar Dalibai a Jiharsa Kyauta Ba Ko Kobo

Abba Gida Gida ya amince da biyan kudin jarabawar dalibai 55,000 a Kano
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf. Hoto: The Daily Reality.
Asali: Facebook

A wata sanarwar da sakataren yada labaransa, Sunusi Bature ya fitar a ranar Lahadi 18 ga watan Yuni, ya ce gwamnan ya roki daliban da su dage don samun sakamako mai kyau.

Ya kara da cewa kokarinsu shi zai ba wa gwamnati tabbacin kara himma wurin zuba kudade a harkar ilimi don samun abun da ake bukata, cewar Daily Trust.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abba Gida Gida ya amince da biyan kudin jarrabawar dalibai 55,000

A cewar sanarwar:

"A matsayin mu na gwamnati da ta damu da al'umma musamman a harkar ilimi, mun amince da biya wa dalibai 55,000 kudin jarrabawa a jihar.
"Ya kamata ku saka himma don samun sakamako mai kyau da zai saka iyayenku da gwamnati alfahari da ku."

Abba ya ba da tabbacin ci gaba da gyara harkar ilimi

Gwamnan ya bai wa 'yan jihar tabbacin cewa zai ci gaba da kawo sabbin tsare-tsare don inganta harkar ilimi a jihar baki daya, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

EFCC Ta Sanar da Sabon Shugaban Rikon Kwarya Bayan Tinubu Ya Dakatar da Bawa

Abba Gida Gida Ya Yi Magana Kan Dawo da Korarren Sarki Sanusi

A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa har yanzu bai yanke hukunci kan Sunusi Lamido ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin kore jita-jitar da ke kawo cewa zai dawo da korarren sarki Sunusi mukaminsa.

Abba Kabir har ila yau, ya ce bai shirya wani abu ba kan rusa sabbin masarautun da tsohon gwamna Ganduje ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.